2023: Ɗan Takarar Gwamna Ya Fice Daga PDP, Ya Koma Bayan Peter Obi Na LP
- Tsohon ɗan takarar gwamnan Anambra, Valentine Ozigbo, ya tabbatar da ficewarsa daga PDP a wani taro jiya
- Ozigbo, ya ce ba zai iya raba jam'iyya tsakaninsa da Peter Obi ba, wanda ya kira ɗan uwansa, uban gidansa kuma jagora
- Ƙura ta daɗa turnuƙe babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP, musamman tsakanin Atiku da Wike
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Anambra - Tsohon ɗan takarar gwamna a inuwar PDP a zaɓen gwamnan Anambara 2021, Valentine Chineto Ozigbo, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar Labour Party (LP) yayin da ake tunkarar zaɓen 2023.
Jigon PDP ya bayyana sauya shekarsa a hukumance ne a wurin wani taro na musamman da ya gudana ranar Talata a Anambra, wanda ya samu halartar ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi.
Da yake bayyana cigaban a shafinsa na Facebook, Ozigbo ya ce matakin shiga LP bai ba shi wahala ba domin ya samu nutsuwa da soyayya a jam'iyyar.
Ya kuma bayyana Peter Obi a matsayin ɗan uwa, aboki, Mai gida, kuma jagora, a cewarsa ba ta yadda za'ai ya iya zama a wata jam'iyya yayin da Obi ke takarar shugaban ƙasa karkashin LP.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wani sashin sanarwan da ya rubuta a shafinsa, Mista Ozigbo ya ce:
"A yau, ɗan takarar mu na shugaban ƙasa, Peter Obi, ya karɓe ni zuwa jam'iyyar LP tare da shugabannin jam'iyyar mu mafi saurin ɗaukaka da yaɗuwa a nahiyar Afirka karkashin jagorancin shugaban LP na ƙasa, Dr. Julius Abure."
"Shiga LP shi ne abu mafi sauki a wuri na saboda a jam'iyyar ne na samu natsuwa da soyayya. Ina matukar godiya da jin daɗin yadda aka tarbe ni da tawagar tafiyar siyasa ta karkashin Chief Toni Offiah."
"Duba da alaƙata da mai girma Obi a matsayinsa na babban yayana, uban gidana, abokina kuma jagora na, ba zai yuwu yana neman kujerar shugaban ƙasa, ni kuma ina wani wuri daban ba. Nan ne gidana, ina jaddada cewa ni cikakken Obidient ne 100%."
Wani Ɗan takarar shugaban ƙasa ya duƙa gaban Obasanjo
A wani labarin kuma Hoto Ya Bayyana, Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Najeriya Ya Duƙa Har Kasa Gaban Obasanjo
Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarashin jam'iyyar Accord Party ya kai ziyarar girmama wa ga tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta.
Farfesa Christopher Imumolen, ɗan takarar kujera lamba ɗaya ya shiga jerin waɗan da suka gana da Obasanjo a katafaren gidansa da ke jihar Ogun.
Asali: Legit.ng