Na Hannun Daman Tsohon Ministan Buhari Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

Na Hannun Daman Tsohon Ministan Buhari Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ta yi babban rashi na jigonta da ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP
  • Princewill Diike, wanda na hannun daman tsohon minsitan Sufuri ne, ya ce bai ga ta zama ba a jam'iyyar APC
  • Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya ce mutane na ta tururuwar komawa PDP, sun kashe adawa baki ɗaya a jihar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Jigon jam'iyyar All Progressive Congress wato APC a jihar Ribas, Princewill Diike, ya yi hannun riga da jam'iyyar, ya koma PDP.

Mista Diike, makusanci ne ga tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce ya tattara kayansa ya bar APC ne saboda an yi watsi da gargaɗin da yake na matsalar da ke tunkaro jam'iyyar a Ribas.

Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi.
Na Hannun Daman Tsohon Ministan Buhari Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP Hoto: punchng
Asali: UGC

Jaridar Punch ta tattaro cewa Amaechi da Diike, duk sun fito ne daga garin Ibima da ke ƙaramar hukumar Ikwerre, jihar Ribas.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisu Biyu da Dubbannin Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Arewa

Diike, Lauya masanin doka ya rike mukamin mashawarci na musamman kan harkokin ɗalibai lokacin Amaechi na kan kujerar gwamnan Ribas, ya ce duk shawarin da ya bayar na yadda za'a ceto APC an binne su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyasa ya zaɓi shiga jam'iyyar PDP?

Tsohon jigon APC ya ce ya yanke haɗa inuwa ɗaya da gwamna Nyesom Wike ne saboda ya yi abin a zo a gani a Ribas, musamman a bangaren ayyukan cigaba na raya ƙasa, This Day ta ruwaito.

A kalamansa ya ce:

"Jam'iyyar siyasa hanya ce ta zuwa kan madafun iko, lokacin da na fahinci APC ta kama hanyar rushe wa, sai na fara ankarar wa, abun mamaki sai suka aaida ni tamkar manzon azaba."
"Duk da haka ban daina kokawa ba, da kuma ba da shawarin hanyar warware matsaloli ba amma jam'iyya ta yi kunnen uwar shegu da ni. Ko kallon shawarwari na basu yi, don me zan cigaba da zama jam'iyyar da ta kama hanyar rushe wa?"

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Shugaban APC Na Jiha Ɗaya Ya Rasa Muƙaminsa, An Kore Shi Daga Jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta gano cewa jam'iyyar APC na fama da ɓarakar yawan murabus ɗin ƴaƴanta, yayin da wasu ke koma wa inuwar jam'iyyar PDP a jihar Ribas.

A wani labarin kuma Majalisar Shura ta gindaya wa Mallam Shekarau Sharuɗɗa 5 Kafin Ya sauya Sheka zuwa PDP

Majalisar koli dake ya ke hukunci a ɓangaren Mallam Shekarau ta gindaya wa Sanatan wasu sharuɗɗa kafin ya koma PDP.

Hakan na zuwa ne biyo bayan jita-jitar da ke yawo cewa Atiku Abubakar da Bola Tinubu na zawarcin tsohon gwamnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel