Tikitin Musulmi da Musulmi: Matar Tinubu ce Zata Zama Babbar Faston Cocin Aso Rock, Keyamo

Tikitin Musulmi da Musulmi: Matar Tinubu ce Zata Zama Babbar Faston Cocin Aso Rock, Keyamo

  • Mai magana da yawun tawagar kamfen din shugabancin kasa na APC, Festus Keyamo, yace matar Tinubu zata zama babbar faston cocin Aso Rock
  • Ya bayyana cewa, wasu daga cikin 'ya'yan Tinubu duk Kiristoci ne kuma ya matukar hidimtawa addinin a lokacin da yake gwamnan Legas
  • Keyamo yace, tikitin Musulmi da Musulmi da APC tayi ba cin fuskar Kiristoci bane, hanya ce da jam'iyyar ta kawo na lashe zabe

FCT, Abuja - Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da aikin yi, yace Oluremi Tinubu, matar 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, ita ce zata jagoranci cocin Aso Rock idan mijinta ya zama shugaban kasa.

Ministan ya sanar da hakan ne a wani shirin siyasa da aka tattauna da shi a Channels TV a ranar Talata.

Kayemo, wanda shi ne mai magana da yawun kwamitin kamfen din Bola Tinubu, ya yi wannan tsokacin ne yayin martani kan batun tikitin Musulmi da Musulmi na jam'iyyar, TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Masoyin Inyamurai ne: Jigon NNPP ya fadi abin da Kwankwaso ya shirya yiwa Inyamurai

Festus Keyamo
Tikitin Musulmi da Musulmi: Matar Tinubu ce Zata Zama Babbar Faston Cocin Aso Rock. Hoto daga theCabel.ng
Asali: UGC

Tinubu ya zabo Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno kuma Musulmi, a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan cigaban ya janyo cece-kuce daga masu ruwa da tsaki ballantana Kungiyar Kiristoci ta kasa, CAN.

Amma Keyamo yace wannan hukuncin wani irin tsari ne jam'iyyar da ta fitar domin lashe zaben shugabancin kasa 2023.

Yace 'dan takarar shugabancin kasan da iyalinsa suna da addinai daban-daban.

"Wannan bashi da wata alaka da hadin kai, wannan hanya ce ta samun nasara," yace.
“Wannan ba cin zarafin Kiristoci bane. Musulmai sune marasa rinjaye a kudu kuma Asiwaju Musulmi ne daga kudi. Wasu Musulman sune marasa rinjaye a arewa.
"Kamar yadda nace, ku kalla Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shi kadai. Ku kalla tarihin da ya kafa, shi ya dawo da makarantun kiristoci hannunsu a Legas lokacin yana gwamna.
“A game da coci, shi ya mayar musu da makarantunsu. Shi ya gina wuraren bautar addinai daban-daban. Wasu daga cikin 'ya'yansa Kiristoci ne, matarsa fasto ce.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnonin Najeriya sun ba lallai a yi zabe a wasu jiohohin Arewa ba a 2023

“Cocin fadar shugaban kasa matarsa zata dinga amfani da ita saboda ita ce zata zama babbar faston wurin. A saboda haka ba za arufe cocin ba. Za a dinga amfani da ita idan Ubangiji ya yarje masa ya zama shugaban kasa."

Ministan Buhari Yace Zai Iya Tuka Mota daga Abuja Zuwa Kaduna Ba Jami'an Tsaro

A wani labari na daban, Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da aikin yi, yace zai iya tuka mota tun daga Abuja har Kaduna ba tare da masu tsaron lafiyarsa ba.

Keyamo ya sanar da hakan ne a ranar Talata a wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin na Channels.

Tafiyar mai nisan kilomita 155 kan babbar hanyar tana daya daga cikin titunan dake da hatsari kuma ake fuskantar manyan farmakin 'yan ta'addan dake tare mutane tare da garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng