Wasu Miyagu Sun Kai Farmaki Kan Magoya Bayan Atiku Abubakar a Jihar Ribas
- Wasu yan daba sun tarwatsa ɗakin taron da aka shirya domin tabbatar da goyon bayan Atiku Abubakar a jihar Ribas
- Wata ƙungiya ta shirya taro a garin Bori, ƙaramar hukumar Khana da Ribas da nufin bayyana wa duniya mubaya'arta ga Atiku
- Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da Atiku na takun saƙa da juna tun bayan kammala zaɓen fidda gwanin PDP
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Rivers - Wasu tsageru da ake zargin Yan daba ne kuma magoya bayan jam'iyyar PDP sun tarwatsa taron ƙungiyar National Mandate Group (NMG) ranar Lahadi a jihar Ribas.
Leadership ta rahoto cewa ƙungiyar NMG na goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a babban zaben 2023 da ke tafe.
An tattaro cewa ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Sanata Lee Maeba, ta shirya gudanar da taronta a Bori, hedkwatar ƙaramar hukumar Khana, a wani wuri mallakin tsohon Sanatan gabanin yan Daban su farmake su.
Haka zalika, bayanai sun tabbatar da cewa ƙungiyar ta shirya taron ne nufin tabbatar da mubaya'arta ga Atiku, wanda yanzu haka ba ya ga maciji da gwamna Nyesom Wike na Ribas.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rikici ya shiga tsakanin gwamna Wike da Atiku ne tun bayan zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa da kuma matakin zaɓen gwamna Okowa a matsayin ɗan takarar mataimaki.
Gwamna Wike ya jaddada kudirinsa kan gidajen Mai
Gwamnatin Ribas karkashin gwamna Wike ta jaddada kudirinta na cafke tare da hukunta duk wani mai gidan Mai da ke siyan Man Fetur hannun ɓarayi masu satar ɗanyen mai su tace.
Ta ce babu wata suka da zata dakatar da ita daga hukunta ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Patakwal II a majalisar wakilan tarayya, Hon. Chinyere Igwe, wanda tuni aka garƙame gidan Mansa bisa zargin haramtacciyar harkallan mai.
Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Ribas, Chief Emeka Woke, shi ne ya bayyana haka a ƙaramar hukumar Gokana ranar Litinin a wurin taron wayar da kai kan muhimmancin katin zaɓe.
Woke ya jaddada cewa kwansutushin ya baiwa gwamnatin jiha cikakken ikon ɗaukar mataki kan duk wanda ya tsoma hannu a harkokin kashe tattalin arzikin kasa.
A wani labarin kuma Shura Ta Gindaya Wa Malam Shekarau Sharudda 5 Idan Zai Sauya Sheka Zuwa PDP
Majalisar koli dake ya ke hukunci a ɓangaren Mallam Shekarau ta gindaya wa Sanatan wasu sharuɗɗa kafin ya koma PDP.
Hakan na zuwa ne biyo bayan jita-jitar da ke yawo cewa Atiku Abubakar da Bola Tinubu na zawarcin tsohon gwamnan.
Asali: Legit.ng