Kwankwaso Mayaudari Ne, Ya Yaudaremu, Inji Tsohon Gwamnan Kano Shekarau
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa, jagoran NNPP ya yaudare shi da sauran masoyansa
- Kwankwaso ya jawo Shelarau zuwa jam'iyyar NNPP mai alamar kayan marmari a wannan shekarar ta 2022
- Ana ta rade-radin cewa, jigon siyasar jihar Kano, Shekarau zai bar NNPP zuwa jam'iyyar PDP ta su Atiku
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Kano - Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana yadda Sanata Rabiu Kwankwaso, ya yaudare shi da ma magoya bayansa bayan da ya jawo su zuwa jam'iyya mai kayan marmari ta NNPP a watan Mayu.
Shekarau da Kwankwaso dukkansu tsoffin gwamnoni ne a Kano, jiha mafi tashen kasuwanci a Arewa maso Yammacin Najeriya, Leadership ta ruwaito.
A yau Litinin, 22 ga watan Agusta, Shekarau ya shaida wa manema labarai cewa, zai bayyana matsayinsa na yiwuwar sauya sheka da NNPP zuwa wata jam'iyyar nan ba da jimawa ba.
A halin yanzu, Shekarau ne wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa kuma tsohon jigo ne a jam'iyyar APC mai mulki, rahoton Tribune Online.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Nan kusa zan fadi matsaya ta
Da yake bayani ga manema labarai,ya ce ya gana da kwamitinsa na Shura a karshen mako, inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafi makomai siyasar Atiku Abubakar da kuma yiwuwar komawar Shekarau PDP.
Barista Habib Shehu, wanda shine jagoran kwamitin na shura an ce ya ba da rahotonsa domin duba da kuma yanke shawarar karshe.
Ya zuwa yanzu dai Shekarau bai bayyana PDP zai koma ba, amma ana ta rade-radin tawagar Atiku na bin kafa domin zawarcin jigon siyasar zuwa PDP.
Zan Mika Jami’o’in Tarayya Ga Gwamnatin Jihohi, inji dan takarar PDP Atiku
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce zai sauya akalar rikon jami’o’in gwamnatin tarayya, inda zai ba gwamnatin jihohi ragamarsu.
Atiku ya bayyana haka ne a yau Litinin 22 ga watan Agusta a bikin bude taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya na 2022 da aka gudanar a Otal din Eko and Suites da ke Legas a Kudu maso Yamma.
Da yake bayyana dalilinsa na kudurin mika jami'o'in Najeriya ga gwamnatocin jihohi, ya ce gwamnatin Najeriya ba ta da isassun kayan aikin ci gaba da rike jami'o'i, rahoton TheCable.
Asali: Legit.ng