Tsagin Malam Shekarau Ya Gindaya Sharudda 5 Na Sauya Sheka Zuwa PDP

Tsagin Malam Shekarau Ya Gindaya Sharudda 5 Na Sauya Sheka Zuwa PDP

  • Majalisar koli dake yanke hukunci a ɓangaren Mallam Shekarau ta gindaya wa Sanatan wasu sharuɗɗa kafin ya koma PDP
  • Hakan na zuwa ne biyo bayan jita-jitar da ke yawo cewa Atiku Abubakar da Bola Tinubu na zawarcin tsohon gwamnan
  • Bayanai sun ce Atiku ya yi wa Shekarau tayin wasu manyan muƙamai idan har ya kafa gwamnati a 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Majalisar Shura mafi kololuwa wajen yanke hukunci kan harkokin siyasar gidan Shekarau, ta gindaye Sharuɗɗa biyar gabanin sauya sheka daga NNPP zuwa PDP.

Daily Nigerian ta rahoto cewa sharuɗɗan na cikin rahoton da Shura da miƙa wa tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ranar Asabar da ta gabata.

Rahotanni sun nuna cewa Malam Shekarau ya fara shirye-shiryen sauya sheƙa daga NNPP ta su Kwankwaso zuwa PDP duk da yana da tikitin takarar Sanatan jam'iyya mai kayan maramari a hannu.

Kara karanta wannan

Kai mayaudari ne: Shekarau ya dira kan Kwankwaso, ya fasa kwai kan maganar sauya sheka

Malam Ibrahim Shekarau.
Tsagin Malam Shekarau Yan Gindaya Sharudda 5 Na Sauya Sheka Zuwa PDP Hoto: dailynigerian
Asali: Twitter

Lokacin da Shekarau ya baje tattaunawar da yake yi da Atiku Abubakar da tayi mai gwabi da ya masa ga majalisar Shura, wasu majiyoyi daga gidan sun ce kawuna sun rabu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da gabatar da batun sauya sheƙar a gaban Shura, hakan bai hana tsohon gwamnan ya nemi shawarin majalisar gabanin ya yanke hukunci na ƙarshe.

Wake tayi Atiku ya yi wa Shekarau?

Wata majiya mai karfi ya shaida wa Daily Nigerian cewa a yunkurin jawo hankalin Shekarau, Atiku ya yi alƙawarin naɗa shi Sakataren gwamnatin taraya ko shugaban ma'aikatan gidan gwamnati.

Haka zalika, Shekarau ne zai jagoranci tawagar yakin neman zaɓen Atiku na shiyyar arewa maso yamma, tare da maida hankali wajen samun goyon bayan Malaman Addini da Sarakuna.

Wane sharudda Shura ta gindaya?

A makon da ya gabata, Ɓangaren Shekarau ya kafa kwamitin mutum 21 da zai yi nazari kan tayin Atiku sannan kuma ya gabatar da rahoto kan cigaban da aka samu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Kaduna Ya Magantu Kan Shirin Tsige Gwamna El-Rufai

Kwamitin wanda aka faɗaɗa shi zuwa mutum 30, ya zauna kan lamarin, kana ya cimma matsayar wakilta mutum biyar da zasu kafa, 'Sharudda da ƙa'idoji"

"Manyan sharuɗɗa a cikin guda biyar ɗin sune; Wajibi mambobin Shura su shiga duk wata gana wa da Tinubu ko Atiku nan gaba da kuma; Mallam ba zai sauya sheƙa ba sai an yi yarjejeniya mai karfi da Tinubu ko Atiku ta naɗa mambobin Shura wasu muƙamai."
"Zan iya tuna cewa waɗan nan batutuwa 2 sune manya a cikin sharuddan. Yanzun an wuce babin Malam kaɗai za'a naɗa, tilas a haɗa da magoya bayansa. An shirya waɗan nan sharudda ne don guje maimaita kuskuren baya."
"A baya Malam ya sauya sheka zuwa PDP, APC yanzu kuma ga NNPP ba tare da gindaya buƙatun mutanen da ke tare da shi ba kamar samun tikiti ko naɗa su mukaman siyasa."

- Inji wata majiya mai alaƙa da sharuddan.

Kara karanta wannan

Jiga-Jigai da Mambobin PDP Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC, Shugabar Mata Ta Rungume Su a Kaduna

Wani makusancin Shekarau da ya nemi a sakaya bayanansa ya shaida wa jaridar cewa Matsin lamba daga wasu yan arewa da mutanen da ke tare da sanatan ne suka matsa wa Malam ya koma PDP.

"Yayin da Malam Shekarau ke kokarin shawo kan rikicin cikin gida, wasu dattawan arewa sun fara kiran ya haɗa hannu da Atiku."

A wani labarin kuma 'Sako Daga Allah' Wani Babban Malami ya faɗi sunan ɗan takarar da zai gaji Buhari a 2023

Wani Malami ya bayyana maganar Manzanci cewa ɗan takarar APC, Bola Tinubu, ne zai gaji shugaba Buhari a zaɓen 2023.

A shekarar 2019, Malamin Cocin ya yi hasashen shugaba Buhari zai lashe zaɓe karo na biyu, haka Sanata Omo-Agege.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262