2023: Jigon Jam'iyyar APC A Arewa Ya Sauya Sheka Zuwa Labour Party Ta Peter Obi, Ya Bayyana Dalili
- Kamaludeen Shehu Musa, jigon jam'iyyar APC ya fito fili ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar ya koma Labour Party gabanin 2023
- Musa ya yi zargin cewa jam'iyyar ta APC bata cika alkawurran da ta dauka wa yan Najeriya ba yayin zaben 2015
- Ficewar na jigon jam'iyyar APC ya zo ne a lokacin da Labour Party ta samu kyautan ofishin kamfen daga hannun wani magoyin bayanta a Owerri
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Twitter - Wani jigo a jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Kamuludeen Shehu Musa, ya fice daga jam'iyyar mai mulki ya shiga Labour Party, gabanin babban zaben 2023.
Musa wanda ya nuna katinsa na APC a shafinsa na Twitter ya zargi tsohuwar jam'iyyarsa da gaza cika alkawurran da ta yi wa yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikicin Atiku Da Wike: "Shedan Ya Shigo Jam'iyyar Mu", Jigon Jam'iyyar PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Yi Gargadi
"Na kasance dan jam'iyyar APC mai kati! Na goyi bayan jam'iyyar saboda tsare-tsarenta, amma, abin takaici sun gaza cika alkawurran da suka dauka, hakan yasa na canja ra'ayi na fara goyon bayan Peter Obi domin a zuciya ta ina ganin shine dan takara wanda ya dace. Fully Obidient and Yusful."
Mutane da dama cikin magoya bayan LP sun yi wa Musa maraba da zuwa sabuwar jam'iyyar a Twitter, wasu sun bashi shawarar ya yi amfani da kwarewarsa na siyasa ya ga cewa jam'iyyar ta samu kuri'u.
An bawa jam'iyyar LP kyautan ofishin kamfen gabanin zaben 2023 a Imo
Hakazalika, an bawa jam'iyyar ta Labour Party kyautan ofishin yakin neman zabe gabanin babban zaben 2023 a Jihar Imo.
Dr Libo Agwara, wani magoyin bayan jam'iyyar a jihar ta kudu maso gabas ne ya bada ofishin matsayin tallafinsa kuma Peter Obi ya kaddamar da ofishin.
Jerin Manyan Mukamai 15 Masu Gwabi Da El-Rufai Da APC Ta Arewa Maso Yamma Suka Nema Daga Wurin Tinubu
Da ya ke magana wurin kaddamar da ofishin, Obi ya ce:
"Tafiyarmu ba irin ta sauran bane, za mu dawo da Najeriya. Za mu karbi Najeriya mu mika muku matasa. Za mu iya canja kasar nan, ba zai yi wu a cigaba haka ba."
Asali: Legit.ng