Cikin Sauki Jam'iyyar APC Zata Lashe Zaben 2023, Gwamna Masari

Cikin Sauki Jam'iyyar APC Zata Lashe Zaben 2023, Gwamna Masari

  • Gwamnan Aminu Masari na jihar Katsina ya ce masu cewa APC ba zata kai labari ba a 2023 zasu sha kunya
  • Gwamnan ya kaddamar da ɗakin kwanan ɗalibai da aka raɗa wa sunansa a jami'ar Al-Hikmah da ke jihar Kwara
  • A cewarsa, kalubalen da Najeriya ke fama da su sun shafi duniya, ya kamata kowa ya san yana da rawar da zai taka

Kwara - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce jam'iyyar All Progressive Congress APC ba zata sha wahala ba zata lashe babban zaben 2023 da ke tafe.

The Cable ta ruwato cewa Masari ya yi wannan furucin ne a wurin kaddamar da ɗakin kwanan ɗalibai da aka raɗa wa sunansa a Jami'ar Al-hikmah da ke jihar Kwara ranar Laraba.

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari.
Cikin Sauki Jam'iyyar APC Zata Lashe Zaben 2023, Gwamna Masari Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Gwamnan ya ce waɗan da ke faɗin zai yi wahala Jam'iyyar APC ta kai bantenta a zaɓe mai zuwa, "Ba su san me suke faɗa ba kwata-kwata."

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da Yasa NNPP Ba Zata Iya Cika Wa Shekarau Bukatarsa Ba, Kwankwaso

Masari ya ce abubuwan da Najeriya ke fama da su lamari ne na duniya kuma wasu kasashen duniya na fama da makamantan irin waɗan nan matsalolin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Masu cewa zai wuya jam'iyyar APC ta lashe zaɓe mai zuwa, ba su san abinda ke fita daga harsunan su ba kwata-kwata," inji gwamnan, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

"Haka suka dinga faɗa a zaɓen 2019 cewa APC zata riga rana faɗuwa saboda yanayin da Najeriya ta tsinci kanta, kuma zaɓen ya zo ya nuna musu ba kan dai-dai suke ba."
"Muhimmin abin da ya kamata mu sani shi ne abubuwan da ke damun Najeriya ya shafi duniya, baki ɗaya duniya na fama da rikice-rikice da tashin farashi. Amurka na fama da tashin farashi mafi muni shekara 40."

Kowa na da rawar da zai taka - Masari

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Nake Hana Mijina Damar Saduwa da Ni, Matar Aure Ta Faɗa Wa Kotu

Gwamna Masari ya ƙara da cewa kowane ɗan ƙasa na da gudummuwar da zai iya bayarwa wajen shawo kan ƙalubalen da suka dabaibaye ƙasar nan.

"Ina kallon wannan abun a matsayin wani abu da zai zo ya wuce a tafiyar samun cigaba. Ƙasashen da suka shekara 400 har yanzu suna fama da rikici."
"Kamata ya yi mu rika yi wa shugabannin mu Addu'a, su yi abinda ya dace. Amma kowannen mu na da rawar da zai taka da gudummuwar da zai bayar."

A wani labarin kuma Wani ɗan jam'iyyar APC ya bindige mutum hudu a babban shagon 'Supermarket'

Wani mutumi da ake tsammanin ɗan daban siyasa ne ya bindige mutum huɗu a babban shagon Super Market a jihar Ondo.

Ɗan daban wanda ake wa laƙabi da, Para, ɗan APC, ya yi kaurin suna wajen yi wa mutane kwace ta dole a yankin karamar hukumar Idanre.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani Ɗan Jam'iyyar APC Ya Bindige Mutum Hudu a Babban Shagon 'Supermarket'

Asali: Legit.ng

Online view pixel