2023: Ɗan Gani Kashenin Amaechi Ya Sauya Sheka Zuwa PDP a Ribas

2023: Ɗan Gani Kashenin Amaechi Ya Sauya Sheka Zuwa PDP a Ribas

  • Na hannun daman tsohon ministan Sufuri kuma kakakin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas, Chris Finebone, ya sauya sheka zuwa PDP
  • Wannan cigaban na zuwa ne a lokacin da gwamna Wike na Ribas ya fara ɗasawa da wasu jiga-jigan APC
  • Mista Finebone ya kasance shahararren mai sukar Wike da gwamnatinsa, ya ziyarci gwamnan bayan koma wa PDP

Rivers - Kakakin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas kuma makusanci, ɗan amutun tsohon ministan Sufuri Rotimi Amaechi, wato Chris Finebone, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP.

Finebone, wanda ya shafe tsawon shekarau a matsayin kakakin APC reshen jihar Ribas, ya tabbatar da sauya sheƙarsa ga jaridar Daily Trust da safiyar yau Jummu'a.

Sai dai tsohon jigon APC bai faɗi maƙasudin sauya sheƙarsa ba, a cewarsa, "Ɗan takarar gwamnan Ribas na PDP, Similanayi Fubara, ɗan uwana ne, kusan haka ku zauna lafiya."

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Gwamnan APC Ya Faɗi Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Ɗayansu Ya Gaji Buhari a 2023

Tsohon kakakin APC, Chris Finebone.
2023: Ɗan Gani Kashenin Amaechi Ya Sauya Sheka Zuwa PDP a Ribas Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Jim kaɗan bayan sauya sheƙarsa, Finebone ya ziyarci gwamna Nyesom Wike a gidansa da ke hanyar Ada George, Patakwal tare da rakiyar tsohon shugaban APC, Davis Ikanya, da ɗan takarar gwamna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar Punch ta rahoto cewa Finebone ya yi ƙaurin suna wajen sukar Wike ta kowane fanni, amma sai gashi sun gana da juna a gidan gwamnan ranar Alhamis da yamma.

Da aka tuntuɓe shi ta wayar salula, Finebone ya ce: "Eh gaskiya ne, jiya haka ta faru," amma ya ƙara da cewa zai bayyana dalilinsa nan ba da jimawa ba.

Wike ya fara ƙawance da APC

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wannan cigaban na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamna Wike na Ribas ya fara haɗa kawance da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC.

Indai ba'a samu wani canji a lokacin karshe ba, Kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ribas yau.

Kara karanta wannan

Kokarin Ɗinke Barakar PDP Ya Gamu da Cikas, Shugabar Mata da Daruruwan Mambobi Sun Koma APC

A farkon makon nan, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Ribas, da Sanata Aliyu Wamakko, dukkan su manyan jiga-jigan APC sun kaddamar da ayyukan Wike a jihar.

A wani labarin kuma Kokarin Ɗinke Barakar PDP Ya Gamu da Cikas, Shugabar Mata da Daruruwan Mambobi Sun Koma APC

Jam'iyyar APC a jihar Kebbi ta kara karfi tare da sauya sheƙar wasu ɗaruruwa mambobin PDP a shiyyar Kebbi ta tsakiya.

Shugabar Matan PDP ta shiyyar, Yar Sakkwato Jega, tare da wasu ɗaruruwan masoyanta sun rungumi tsintsiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel