Jam'iyyar ADC Ta Goyi Bayan Kira Ga Shugaba Buhari Ya Yi Murabus

Jam'iyyar ADC Ta Goyi Bayan Kira Ga Shugaba Buhari Ya Yi Murabus

  • Jam'iyyar ADC ta goyi bayan kiran da ɗan takararta na shugaban ƙasa ya yi ga shugaba Buhari ya yi murabus
  • Dumebi Kachikwu, ya nemi Buhari ya sauka daga kujerar shugaban ƙasa tun da ba zai iya kare rayukan yan Najeriya ba
  • Matsalar tsaro da ta yi wa Najeriya katutu ta jawo wasu daga cikin Sanatoci sun fara tunanin tsige shugaban kasa daga kujerarsa

Abuja - Jagororin jam'iyyar Adawa African Democratic Party watau ADC sun goyi bayan kiran da ɗan takararsu na shugaban kasa, Mista Dumebi Kachikwu, ya yi na shugaba Buhari ya yi murabus.

Channels tv ta ruwaito cewa ɗan takarar ya yi kura ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi murabus daga kujerarsa matuƙar ba zai iya haɓaka tattalin arziki da shawo kan matsalar tsaro da suka addabi ƙasar nan ba.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa A Rikicin PDP, Gwamna Wike Da Atiku Abubakar Sun Cimma Wata Matsaya Ɗaya

ADC ta goyi bayan Buhari ya yi murabus.
Jam'iyyar ADC Ta Goyi Bayan Kira Ga Shugaba Buhari Ya Yi Murabus Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jam'iyyar ADC ta caccaki gwamnatin tarayya kan yanayin yadda ta ɗauki yajin aikin kungiyar Malaman Jami'o'i ASUU wanda ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa tsawon watanni.

Jam'iyyar adawan ta kuma ɗauki alƙawarin tsoma baki da kuma tattauna wa da mambobin ƙungiyar ASUU nan da yan kwanaki masu zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

ADC ta yi wannan furucin ne a wurin taron haɗaka na kwamitin amintattun BoT na jam'iyyar da kuma kwamitin gudanarwa na ADC ta ƙasa.

Kachikwu ya nemi Buhari ya yi murabus

Jaridar Ripples Najeriya ta rahoto cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Dumebi Kachikwu, ya nemi shugaba Buhari ya sauka daga kujerar shugaban ƙasa saboda tabarbarewar tsaro.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Kachikwu, ya ce Buhari ba shi da kwarewar da zai kare yan Najeriya biyo bayan kai hari cikin sauki kan abun nufi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sojoji Sun Kai Samame Maɓoyar Yan Ta'adda, Sun Halaka Dandazon Su A Jihar Arewa

"Bayan haka kuma, ina kira da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi abin da ya kamata ya yi murabus tun da ba zai iya kare rayukan yan Najeriya ba," Kachikwu ya faɗa a wani sashin sanarwan.

A wani labarin kuma An fallasa wani shirin gwamna Wike, Da yuwuwar zai Yaƙi Atiku ya koma bayan wannan Ɗan Takarar a 2023

Yayin da ake ganin jam'iyyar PDP ta fara shawo kan rikicinta ganin Wike da Atiku sun zauna, wata majiya ta ce akwai matsala har yanzu.

Wani jagora a PDP ya ce gwamna Wike ka iya komawa yana yaƙar Atiku kuma ba zai sauya sheƙa daga jam'iyya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel