Gwamna Fintiri Zai Jagoranci Tawagar Atiku da Zata Rarrashi Wike

Gwamna Fintiri Zai Jagoranci Tawagar Atiku da Zata Rarrashi Wike

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya naɗa gwamnan Adamawa a matsayin shugaban tawagar sulhu da Wike
  • Ahmadu Fintiri, ya tabbatar da cewa kafin babban zaɓen 2023 komai zama tarihi a rikicin Atiku da gwamna Nyesom Wike
  • Wutar rikicin jam'iyyar adawa PDP na cigaba da ruruwa duk da kokarin da masu ruwa da tsaki ke yi na kawo karshenta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Adamawa - An naɗa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, a matsayin wanda zai jagoranci tawagar sulhu ta Atiku Abubakar a wani yunkuri na kawo ƙarshen nuna yatsa tsakanin gwamna Wike da ɗan takarar PDP.

Gwamnan, wanda ya dira filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa da ke Yola a jirgin Max Air, shi ne ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game daa rikicin PDP.

Gwamnan Adanawa, Ahmadu Fintiri.
Gwamna FintirI Zai Jagoranci Tawagar Atiku da Zata Rarrashi Wike Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A rahoton Punch, Ahmadu Fintiri ya ce an naɗa shi shugaban kwamitin sulhu, wanda Atiku ya kafa da nufin kawo karshen sa'insar da ke tsakaninsa da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa a PDP: Wani Ɗan Majalisar Tarayya Ya Fallasa Jiga-Jigan da Suka Haddasa Rikicin Atiku da Wike

Gwamnan, wanda ya bayyana cewa shi ne ya dace da aikin, ya tabbatar da cewa da izinin Allah, zai samar da fahimtar juna tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa da Wike.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya faɗi haka ne bayan ya ɗan taɓa wasa da tsokana da cewa duba da yadda yake ɗasawa da Atiku da Wike, shi ne mutum ɗaya tilo da yake da ya dace ya kawo karshe saɓanin jiga-jigan biyu.

Bugu da ƙari, gwamnan ya ba da tabbacin cewa rikicin da ya hana babbar jam'iyyar hamayya kataɓus zai zama tahiri kafin babban zaɓen 2023.

Haka zalika ya ce alamu sun nuna kwamitin sulhu zai kai ga nasara bayan ganawarsa ta farko da gwamna Wike, inda ya gano wahala da kuma iyakar da aikinsa.

Wike zai yi asara idan bai goyi bayan Atiku ba - Fintiri

Kara karanta wannan

APC Ta Faɗi Sunan Wani Gwamnan PDP Dake da Hannu a Matsalar Tsaron Jiharsa, Ta Nemi a Kayar da Shi a 2023

A cewar shugaban kwamitin sulhun, gwamna Wike ya zuba hannun jari mai daraja a PDP, idan har be goyi bayan Atiku ba ya yi asara.

Fintiri ya ce, "Su waye abokanansa a APC? Shin kuna son gaya mun waɗan nan da suke ɗasawa da Wike suna kaunar shi? Zan iya baku tabbacin jam'iyyar mu zata dawo da kowa kan turba kamin zaɓen 2023."

"Ko Wike ya san cewa ya yi wa kowa zarra wajen zuba jari a PDP, shin zai gudu ya bar ladansa ne? Mun fahimci yana son mutanensa, kuma ina tabbatar muku zamu yi abinda ya dace idan muka zo kan siraɗin domin binne rikicin nan."

A wani labarin kuma Tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya gargaɗi yan Najeriya kan abu ɗaya da zai rusa Najeriya a 2023

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya gargaɗi yan Najeriya su yi karatun ta nutsu wajen zaɓen 2023 da ke tafe.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Jam'iyyar PDP ta dage zaman NEC saboda ta'azzarar rikicin gida

Obasanjo ya ce idan aka yi kuskuren zaɓen shugabanni a zaɓe na gaba, Najeriya ka iya rushe wa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262