Wani Dan Majalisa Ya Fallasa Sirrin Yadda Rikicin Atiku da Wike Ya Fara

Wani Dan Majalisa Ya Fallasa Sirrin Yadda Rikicin Atiku da Wike Ya Fara

  • Ɗan majalisar tarayya daga jihar Ribas, Solomon Bon, ya yi ikirarin cewa na kusa da Atiku ne suka haddasa rikicin PDP tun farko
  • A cewarsa, tun farko sun yaɗa wasu karerayi game da Wike kafin da kuma bayan zaben fidda gwani da nufin rage masa ƙima
  • Kwamitin amintattu sun fara kokarin shawo kan rikicin, inda Atiku da Gwamnan suka gana a gidan tsohon minista

Abuja - Labaran ƙarya ne suka haddasa rashin jituwa tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da gwamnan Ribas, Nyesom Wike, inji wani jigon PDP kuma mamba a majalisar wakilan tarayya.

Honorabul Solomon Bon, mai wakiltar ɗaya daga cikin mazaɓun jihar Ribas a majalisar wakilai, ya ce bayanan ƙarya da wasu na gindin Atiku suka rinƙa yaɗa wa gabanin da kuma bayan zaɓen fidda gwani sun taka rawa a rikicin PDP.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Gwamnan Arewa Ya Maida Ma'ikata 1,699 da Aka Kora Bakin Aikin Su

Wasu daga cikin waɗan nan karerayin a cewar ɗan majalisan shi ne Gwamna Wike bai gamsu da sakamakon zaɓen fidda gwani ba kuma ya so a zaɓe shi abokin takarar Atiku, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rikicin PDP.
Wani Dan Majalisa Ya Fallasa Sirrin Yadda Rikicin Atiku da Wike Ya Fara Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Mista Bon ya ce irin waɗan nan karerayin, "Sun naƙasa gwamna Wike kana suka ɗaga ɗan takarar, wanda dama can shi ke da nasara a zaɓe."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya yi wannan kalaman ne a wata hira da kafar Talabijin Channels TV ranar Litinin yayin da yake martani kan rikicin da ya addabi PDP da yunkurin wasu na rarrashin Mambobin da suka fusata.

Duk da jiga-jigan biyu sun fara yunkurin sasantawa, Mista Bon ya ce da tun farko mutanen Atiku ba su rinka kirkirar karya ba game da Wike, da rikicin bai kawo yanzu ba.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Sunayen Jihohi 20 da Jam'iyyar APC Ka Iya Shan Kaye a Zaɓe Saboda Rikici

A bayanansa ya ce:

"Rahoton da aka yaɗa cewa Wike ya fusata da PDP da kuma rashin ɗaukarsa a matsayin ɗan takarar mataimaki duk ƙarya ne. Gwamnan bai taɓa nuna sha'awar zama abokin takarar Atiku ba."
"Bai taɓa nema ba kuma bai je rokon a bashi ba, wannan ita ce gaskiyar da ba zasu faɗa ba. Kawai kamar sun yi yunkurin ɓata shi ne."

Ɗan majalisar ya kara da cewa kujerar shugaban kasa kaɗai gwamna Wike ya nema saboda yana da wani kyakkywan shiri ga ƙasa da yake son aiwatarwa.

Daga ina matsalar ta fara?

Bon ya ce baki ɗaya wannan rikicin ya fara ne da, "Rashin kyakkyawan imani. Gwamna Wike bai taɓa cewa bai ji daɗin nasarar Atiku ba," kuma babu dalilin da zai ƙi goyon bayansa.

Tsohon kakaki yaƙin neman zaɓen PDP, wanda ya halarci tattaunawar, Phrank Shuaib ya ce rikicin da ya mamaye jam'iyyar duk takun siyasa ne, "Ba abinda ya fi karfin a shawo kansa."

Kara karanta wannan

Matakai 33 da Gwamnoni Suka Shawarci Buhari Ya Ɗauka Don Ceto Najeriya Daga Durkushewa

Ya kuma maida wa Bob martani kan kalamansa da cewa Atiku bai taɓa tura ko mutum ɗaya ya dankwafar da gwamna Wike ba.

A wani labarin kuma Atiku ya shirya babban gangami, zai tarbi jiga- Jigai da mambobin APC 1,615 da suka koma PDP

Mambobin jam'iyyar APC sama da dubu ɗaya sun sauya sheƙa zuwa babbar jam'iyyar hamayya PDP a jihar Adamawa.

A cewar wakilan masu sauya sheƙan ba su kenan ba, sun kai mutum 6,000 da suka yanke barin APC saboda gazawar Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel