Miyetti Allah ta ce tsohon gwamnan jihar Aanambara Yana wakiltar Kungiyar Biyafra
- Kungiyar Miyetti Allah ta ce ta umurci kowane Bafulatani a Najeriya da da kada ya kuskura ya zabi Peter Obi
- Miyetti Allah ta ce duk Bafulatanin da ya zabi Peter Obi baya kishin mutanen sa kuma ya bukaci a duba tunanin sa
- Sakatare-Janar na kungiyar Miyetti-Allah ya zargi Peter Obi da ruguzawa Hausawa da Fulani kasuwancin su a lokacin da yake gwamnan jihar Anambara
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kungiyar Miyetti Allah ta ce ta umurci kowane Bafulatani a kasar nan da kada ya zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Mista Peter Obi, Rahoton PUNCH.
Miyetti Allah ta ce Obi mutum ne mai nuna kabilanci karara kuma yana wakiltar ra’ayin yan kungiyar Biyafara wanda mulkin sa ba zai kari Fulani da komai ba.
Sakatare-Janar na kungiyar al’adun Fulani ta kasa, Mista Saleh Ahassan, a wata hira da yayi da Sunday PUNCH, ya bayyana cewa, Obi baya cikin jerin mutanen da za su marawa baya a zabe mai zuwa.
Saleh Alhassan, ya ce a matsayin su na manya sun san irin mutanen da bai kamata a zaba ba, musamman wadanda suke kira kan su Obi ko OBIdient, duk Bafulatani da ya zabe shi, bashi da kishin mutanen sa kuma dole a binciki tunanin sa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Alhassan ya kuma bayyana cewa lokacin da Obi yake gwamnan jihar Anambra ya ruguza kasuwancin ‘yan arewa, ya kori Hausawa da Fulani da dama kuma yana hana su shiga Anambra.
Da yake mayar da martani, mai magana da yawun kungiyar Peter Obi Support Network, Mista Jones Onwuasoanya, ya ce Obi mai kishin kasa ne wanda muradinsa na 'yan Najeriya ne kawai.
Abu Uku Da Zan Mayar Da Hankali A Kai Idan Na Zama Gwamnan Kaduna - Isa Ashiru
A wani labar kuma, Honorabul Isa Ashiru Kudan, dan takarar gwamna jihar Kaduna Jam'iyyar PDP ya bayyana abubuwa guda uku da za mayar da hankalin sa idan ya zama gwamna. Rahoton BBC
Ashiru Kudan wanda ke takarar gwamnan jihar Kaduna karo na uku yace abun na farko da zai fara ba muhimmanci a jihar shine fannin tsaro.
Asali: Legit.ng