Abu Uku Da Zan Mayar Da Hankali A Kai Idan Na Zama Gwamnan Kaduna - Isa Ashiru
- Honorabul Isa Ashiru Kudan, dan takarar gwamna jihar Kaduna ya bayyana abubuwa guda uku da za mayar da hankalin sa idan ya zama gwamna
- Ashiru ya ce tsabar son ganin ya kawo sauyi a jihar Kaduna ya sa ya nace sai yayi mulkin jihar Kaduna
- Isa Ashiru Kudan ya ce dole ne ya dawo da sarkunan gargajiya da gwamnatin APC ta sauke su dan samun ingantaccen tsaro a jihar Kaduna
Jihar Kaduna - Honorabul Isa Ashiru Kudan, dan takarar gwamna jihar Kaduna Jam'iyyar PDP ya bayyana abubuwa guda uku da za mayar da hankalin sa idan ya zama gwamna. Rahoton BBC
Ashiru Kudan wanda ke takarar gwamnan jihar Kaduna karo na uku yace abun na farko da zai fara ba muhimmanci a jihar shine fannin tsaro.
Ashiru ya kara da cewa matukar son ganin ya kawo canji a jihar Kaduna ne ya sa ya nace sai ya zama gwamna a jihar.
Honorabul Isa Ashiru Kudan, ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da BBC inda ya bayyana kudirorin sa ma jihar Kaduna
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Muhimaman Abubuwa Da Ashiru Yace Zai Yi A jihar Kaduna Sun Hada Da
Gyara matsalar saro, inganta sha'anin noma da kuma samar wa dumbin matasa ayyukan yi a fadin jihar Kaduna.
Sai kuma dangane da wasu sarakunan gargajiya da gwamnatin APC ta sauke su, Isa Ashiru ya ce dole a mayar da su dan samun ingantaccen tsaro a jihar Kaduna.
Bankin Duniya ta Ware N1.8bn Don Gyara Makarantu 614 a Kano
A wani labari kuma, Wani shiri mai suna ‘Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment (AGILE)’ da bankin duniya ke tallafawa fannin ilimi, zata gyara makarantun sakandire na gwamnati 614 akan Naira biliyan 1.8 a jihar Kano.
Mataimakin kodinetan ayyukan na Bankin duniya, Nasiru Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci sauran ma’aikatan da suka kai ziyarar ban girma ga Sarkin Bichi, Nasiru Ado-Bayero, ranar Alhamis a Bichi. Rahoton Premium Times
Asali: Legit.ng