A Yafe Min: Lalong Ya Roki Cocin Katolika Kan Tuntuben Harshe Da Ya Yi Na Tsoma Paparoma A Siyasar Najeriya
- Simon Lalong ya bawa cocin Katolika da mabiyanta hakuri saboda ambaton sunan Paparoma da ya yi yayin da ya ke kare karbar mukamin da ya yi na direktan yakin neman zaben Tinubu
- Gwamnan na Jihar Plateau cikin wata wasika da ya rubutawa cocin Katolika ya ce ya lura ya yi kuskure a jawabin da ya yi yayin kare kansa yana mai cewa ba don raini ko cin mutunci ya ambaci Paparoma ba
- Jigon na jam'iyyar APC ya ce yana fatar yan uwansa kirista kuma mabiya darikar katolika za su fahimce shi kuma su cigaba da ba shi goyon baya a yayin da ya yi alkawarin cigaba da halaye nagari
Gwamna Simon Lalong na Jihar Plateau ya nemi afuwar Cocin Katolika saboda magana da ya fada game da Paparoma a yayin da ya ke kare nadinsa a matsayin direkta janar na kamfen kungiyar kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, Daily Trust ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da ya ke yi wa manema labari jawabi a Aso Rock, ranar Talata, Lalong ya ce shi haifafan dan darikar katolika ne kuma an masa baptisma kuma fafaroma ya bashi lambar yabo mafi girma, wato 'Knight of Saint Gregory the Great' kuma paparoma bai fada masa kada ya karbi nadin ba, don tikitin musulmi da musulmi ne.
Wannan maganan da ya yi ta janyo cece-kuce da suka musamman daga mabiya darikar Katolika wadanda suka soke shi saboda sako sunan paparoma a siyasa.
Nan take suka bukaci a dakatar da shi daga cocin saboda zargin batanci.
Lalong ya rubuta wasikar neman afuwa
Amma cikin wata wasika da ya rubuta wa Cocin Katolika ta hannun Kungiyar Bishops, Lalong ya ce ya amsa laifin cewa ya yi kuskure na jefa sunan paparoma a siyasar Najeriya.
A yayin da ya yi alkawarin zai cigaba da halaye nagari, gwamnan ya nemi yafiya da fahimta daga cocin.
Ya amsa cewa ya yi kuskure a kokarinsa na kare kansa daga wasu da ke neman siyasantar da nadin da aka masa tare da neman nesanta shi daga darikar ta katolika, Pulse Nigeria ta rahoto
Wani sashi na wasikar ta ce:
"Cikin makon nan yayin kare kaina, na ambaci matsayi na Knight a kuma mabiyin darikar Katolika. A yayin hakan, na ambaci Shugaban mu mai tsarki. Na gano cewa hakan kuskure ne kuma ya sosa wa wasu rai tare da kunyata su, musamman mambobin darikar katolika da Knight.
"Na gane cewa abin da na yi ya wuce kima yayin kokarin kare zabin kashin kaina na karbar nadin da aka min, kuma ambaton sunan babanmu mai tsarki don rashin girmamawa bane.
"Ina son bada hakuri tare da neman afuwa da fahimta daga yan uwa na yan katolika ta hannun ku Kwamitin Bishops, iyayen mu kuma jagororin mu."
Lalong ya ce zai cigaba da girmama cocin da yi mata hidima kamar yadda ya saba na tsawon shekaru kuma yana fatan cocin za ta cigaba da basu kwarin gwiwa a harkokin siyasa.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng