Tikitin Musulmi-Musulmi: Shettima Ya Kamata Ya Sauka, Inji Kungiyar ’Yan Arewa
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya zabi Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa
- 'Yan Najeriya da dama na ci gaba da guna-guni saboda hada musulmi da musulmi a tikitin takarar shugaban kasa na APC
- A baya kiristocin APCn Arewa Najeriya ta nemi a tsige Shettima tare da zabo wani kirista dan yankin domin daidaita tsarin dimokradiyya
Najeriya - Wata kungiyar siyasa da zamantakewa ta Arewa ta tsakiya a karkashin inuwar Middle Belt Congress, a ranar Laraba, ta bukaci tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya koma gefe a batun yin takara da Bola Tinubu
Kungiyar ta yi imanin cewa murabus din Shettima zai iya ceto jam’iyyar APC daga bala’in da ke tafe a zaben 2023 mai zuwa nan da watanni bakwai, Punch ta ruwaito.
Shugaban MBC, Mohammed Bilal, wanda ya yi wannan roko a wata ganawa da manema labarai a Abuja, ya ce karbuwar jam’iyyar APC ta ragu tun bayan zabo Shettima a matsayin abokin gamin Tinubu.
A cewarsa, ta hanyar yin tikitin musulmi da musulmi, jam’iyyar APC ta nuna rashin kishi da mutanta addinai ga dimbin al’ummar kasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Don haka MBC ya yi kira ga Shetima da a mutunce ya yi murabus domin dawo da martabar jam'iyyar a idon dimbin 'yan Najeriya.
Yayin da yake bayyana Shetima a matsayin aboki ga mabiya addinin kirista a Najeriya, Bilal ya ce abin takaici ne yadda ya amince ya tsaya takara takara da Tinubu duk da cewa su biyun duk musulmai ne.
Ya ce:
“Hakika tikitin tsayawa takara na Musulmi da Musulmi na jam’iyyar APC yana zuwa ne da batutuwan siyasa.
"Idan har jam’iyyar APC a matsayinta na jam’iyya na son yin tasiri mai ma’ana a zaben shugaban kasa na 2023, to ya dace jam’iyyar ta yi duba kan tsarin da ta ke na tikitin takarar shugaban kasa."
Tikitin Musulmi-Musulmi: Paparoma bai ce na yi kuskuren marawa Tinubu da Shettima baya ba, inji Lalong
Kungiyar, ta ce bai makara ba ga tsohon gwamnan ya fanshi kansa domin amfanin jam’iyyarsa da ma kasa baki daya, tare da bayyana cewa ba zai bata da miliyoyin Kiristoci ba, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.
Kiristocin APCn Arewa Sun Dage Dole a Ba Su Kujerar Mataimakin Tinubu
A wani labarin, kungiyar Kiristocin Arewa ta APC ta yi kira da a maye gurbin Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar a zaben shugaban kasa mai zuwa, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
Tun kafin wannan hargirsi na kiristocin APC 'yan Arewa, an yi ta rade-radin cewa dan takarar APC Bola Ahmed Tinubu (Musulmi) zai zabi dan uwansa Musulmi a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Tinubu ya yi ta maza, ya ayyana Sanata Kashim Shettima (Musulmi) a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, lamarin da ya jawo cece-kuce da hargitsi daga al’ummar Kiristan kasar nan.
Asali: Legit.ng