Buhari Ya Nada Mukami a Gwamnatinsa, An Maye Gurbin Jami’in da ya Rasu a Ofis
- Muhammadu Buhari ya ba Muhammad Sabo Lamido kujerar babban kwamishina a NUPRC
- Idan Majalisa ta amince da nadin, Muhammad Sabo Lamido zai maye gurbin Hassan Gambo
- Hassan Gambo ya rasu bai dade yana rike da wannan kujera a hukumar ta NUPRC a Abuja
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Muhammadu Buhari ya zabi wanda yake so ya zama sabon kwamishina a hukumar Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission.
Mai magana da yawun bakin Shugaban Najeriya, Femi Adesina ya bayyana wannan a jawabin da ya fitar a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta 2022.
Mai girma shugaban kasa ya zabi Muhammad Sabo Lamido ya rike kujerar kwamishinan kudi a wannan hukumar mai kula da harkar mai.
Majiyar VON tace a jiya Shugaba Muhammadu Buhari ya aikawa majalisar dattawan Najeriya takarda mai kunshe da neman nadin Alhaji Sabo Lamido.
Wasikar tace Muhammad Sabo Lamido zai maye gurbin Hassan Gambo wanda ya rasu kwanaki yayin da yake rike da kujerar kwamishinan NUPRC.
Rahoton Sun yace Buhari ya roki Sanatoci su amince da Lamido a matsayin jami’in na NUPRC, kamar yadda suka saba amincewa da duk bukatunsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da zaran Ahmad Lawan ya karanto wannan wasika a zauren majalisa, ake sa ran Sanatoci za su tafka muhawara a tsakaninsu domin a tantance shi.
A watan Afrilun 2022 aka tabbatar da kwamishinonin hukumar bayan an tantance su a majalisa
Kowane yanki a Najeriya yana da wakilci a NUPRC. Lamido zai yi aiki tare da Nuhu Habib, Tonlagha Roland John, Ms Kelechi Ofoegbu da Jide Adeola.
Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission ta na cikin hukumomin da aka samar bayan an yi wasu garambawul wajen harkokin man fetur.
An kafa NURPC ne da nufin tabbatar da cewa ana bin dokoki da ka’idoji wajen sha’anin mai da gas. Hedikwatar hukumar ta na birnin tarayya Abuja.
Rikici kan nadin hukumar NUPRC
Kwanaki ne aka ji labari wani Lauya, Francis Mgbo ya je kotu, yana kalubalantar nadin sababbin shugabannin hukumar NMDPRA da NUPRC da ka yi.
Francis Mgbo ya nemi yayi shari’a da Ministocin man fetur da AGF. A halin yanzu Muhammadu Buhari ne ke rike da kujerar babban Ministan man fetur.
Asali: Legit.ng