2023: APC Ta Samu Babban Tawaya A Yayinda Fitaccen Jigonta Ya Yi Murabus Daga Jam'iyyar
- Wani jigo na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Abia ya fita daga jam'iyyar ya koma jam'iyyar Action Peoples Party, APP
- Sanarwar da dan takarar gwamnan na APP a jihar, Cif Mascot Uzor Kalu, ya fitar ta nuna cewa Cif Princewill Ukaegbu zai sanar da ficewarsa cikin yan kwanaki
- An bayyana jigon na APC a matsayin dan siyasa mai kusanci da talakawa wanda komarsa APP babban riba ne ga Mascot
Jihar Abia - Jigo a jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar Abia, Cif Princewill Ukaegbu ya fice daga jam'iyyar ya koma Action Peoples Party, APP.
Ana fatan Ukaegbu, tsohon shugaban karamar hukumar Umuahia na Arewa zai sanar da sauya shekarsa nan ba da dadewa ba, The Sun ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanarwar daga dan takarar gwamnan na APP a jihar, Cof Mascot Uzor Kalu, ta ce jigon na APC dan siyasa ne mai kusanci da talakawa kuma sauya shekarsa za ta taimaka masa samun nasara, New Telegraph ta rahoto.
Wani sashi na sanarwar ta ce:
"Mascot yana kara fice a takarar gwamna. Zabe ne tsakaninsa da sauran. A zamanin gwamnatin Orji Uzor Kalu kawai aka samu gwamnati mai kyau. Abin da muke da shi yanzu wasan kwaikwayo ne. Lokaci ya yi da za a dawo wa jihar da darajarta."
Ficewar ta Ukaegbu na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban jam'iyyar All Progressives Congress na kasa ya fada wa shugabannin jam'iyyar na jihar Abia su daidaita kansu gabanin zaben 2023.
2023: Rikicin PDP Ya Dauki Sabon Salo, Gwamnoni Da Ke Goyon Bayan Wike Sun Gindayawa Atiku Sabbin Sharruda
A wani rahoton, gwamnonin jam'iyyar PDP da ke biyaya ga gwamnan Rivers, Nyesom Wike, sun bada wasu sharruda ga dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar, kafin su mara masa baya a zaben 2023, kamar yadda aka rahoto.
A cewar Daily Independent, gwamnonin za su hadu da Atiku a karshen mako don tattaunawa kan matsalolin da ke adabar jam'iyyar.
Jaridar ta rahoto cewa daya daga cikin mambobin tawagar Gwamna Wike yana cewa duk ma abin da ya faru, sun amince babu wanda zai fita daga jam'iyyar.
Asali: Legit.ng