Jigon PDP Da Daruruwan Mambobi Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Kebbi

Jigon PDP Da Daruruwan Mambobi Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Kebbi

  • Jam'iyyar PDP ta gamu da sabon koma baya a yunkurinta na kwace mulkin jihar Kebbi daga hannun jam'iyyar APC a zaɓen 2023
  • Jigon PDP a ƙaramar hukumar Maiyama, Alhaji Abubakar Kurun Kuku ne ya jagoranci masu sauya sheƙan zuwa APC
  • Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar da wasu kwamishinoni da hadiman gwamna sun halarci gangamin karɓan mutanen

Kebbi - Wani jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ƙaramar hukumar Maiyama, jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Kurun-Kuku, tare da dandazon magoya bayansa sun sauya sheƙa zuwa APC.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta ruwaito cewa masu sauya sheƙan sun tabbatar da nufin su ne a wurin wani gangamin APC da ya gudana a garin Maiyama ranar Talata.

Taron APC.
Jigon PDP Da Daruruwan Mambobi Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Kebbi Hoto: punchng
Asali: UGC

Daily Trust ta ce Shugabannin jam'iyya da cincirindon magoya bayan APC bisa jagorancin shugaban jam'iyya na jiha, Alhaji Muhammad Kana-Zuru, ne suka tarbi masu sauya sheƙar hannu bibbiyu.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Majalisar Tarayya Na Zango Biyu, Ɗan Takarar Gwamna Da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Sauya Sheka

Meyasa suka sauya sheƙa?

Da yake sanar da komawarsu APC tare da dandazon mambobi, Alhaji Abubakar Kurun- Kuku, ya ce nagarta da salon tafiyar da mulkin jihar Kebbi na gwamna Atiku Bagudu da yadda ya ɗauki matakai lokacin annobar COVID19 ne suka ja hankalin su zuwa APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Mun shigo APC ne saboda mun gamsu da jagoranci mai kyau da gwamnan mu ke yi, cigaban da jihar mu ta yi wanda kowa ke kallo da idonsa da kuma yadda ya jajirce wajen shawo kan tattalin arzikin jiha lokacin Annoba."

Rahoton Vangaurd ya nuna cewa Jigon ya jagoranci mambobin PDP 4,219 sun fice daga jam'iyyar, sun koma APC.

Kun zama ɗaya da kowa - APC

A jawabinsa, ɗan takarar mataimakin gwamna na APC, Sanata Umar Tafida, ya yaba da matakin masu sauya sheƙan duba da cigaban da jam'iyya ta kawo a matakai uku na mulkin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Tsintsiya ta tsinke a Borno: Dan a mutun Tinubu ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Haka nan, shugaban APC a ƙaramar hukumar Maiyama, Alhaji Saidu Giwa-Tazo, ya tabbatar musu da cewa ba za'a nuna musu banbanci ba, sun zama yan gida ɗaya da sauran mambobi.

Ya kuma bayyana tsantsar jin daɗinsa ganin cewa jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Maiyama ta ƙara ƙarfi fiye da lokacin baya.

Daga cikin manyan jiga-jigan da suka halarci gangamin sun haɗa da mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kebbi, Alhaji Usman Ankwai, kwamishinoni da hadiman gwamna.

A wani labarin kuma Kun ji cewa Kwamishinan Gwamnan Sakkwato Ya Bi Sahun Wasu Jiga-Jigan PDP, Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Ɗaya daga cikin kwamishinonin da gwamna Aminu Tambuwal ya maida kan kujerun su ya sauya sheƙa daga APC zuwa PDP.

Kanal Garba Moyi mai ritaya ya bi sahun shugaban ƙaramar hukuma.da wasu Kansiloli da suka koma APC jiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262