El-Rufai: Na Fadawa Tinubu Ban Bukatar Komai a Gwamnatinsa, Bai Yarda Ba

El-Rufai: Na Fadawa Tinubu Ban Bukatar Komai a Gwamnatinsa, Bai Yarda Ba

  • Malam Nasir El-Rufai ya maida martani ga masu tunanin yana kwadayin mukami nan gaba
  • El-Rufai yace shekaru sun fara zuwa masa don haka yake bada shawarar a tafi da wasu matasa
  • Gwamnan na Kaduna yake cewa har yanzu yana rigima da Bola Tinubu, bai son ganin ya huta

Kaduna - A wani bidiyo da yake yawo a dandalin sada zumunta, an ji Gwamna Nasir El-Rufai yana bayanin irin matsin lambar da yake fuskanta.

Da ya yi wani taron zantawa da manema labarai a makon da ya gabata, Malam Nasir El-Rufai ya nuna sam bai da sha’awar kara karbar wani mukami.

Gwamnan na Kaduna yake cewa a shekarunsa (62), ya gaji da rike kujerar gwamnati, amma yace Bola Tinubu ya dage cewa ya zo a cigaba da aiki tare.

Kara karanta wannan

Har yanzu akwai harsashi a ciki na: Bidiyon labarin fasinjan jirgin Abd-Kad a hannun 'yan bindiga

“Ni ba siyasa na fito in yi daga farkon rayuwa ta har karshe ba. Da can kasuwancina nake yi, ina aiki na ne.
Kafin zabe, na fada masa (Tinubu) sarai, domin ya fada mani yana so in taimake sa, nace kwarai duk za mu taimake ka.

Ba na neman komai yanzu

Amma ka sani, babu abin da nake so domin na gaji. Na godewa Ubangiji, wannan wanda nayi, ya isa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai yace sam ban isa ba, kuma ban gaji ba, sai mun sake maganar, nace ai sai muyi tayi, amma ni ba zan yi ba.”
El-Rufai
Malam Nasir El-Rufai da Bola Tinubu Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Akwai masu jini a jika

Tsohon Ministan yake cewa duk abin da ake bukatar ya yi, akwai matasa da ya yi aiki tare da su a gwamnati da za su iya yin wannan aiki tamkar shi ya yi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Bahaushiya Da Ke Tuka Adaidaita Sahu Don Neman Na Kai, Ta Burge Mutane

Malam El-Rufai yace akwai masu sauran karfi, ilmi da jajircewar da zai iya nunawa domin a ba mukamai daga cikin ma’aikata da kwamishonin jihar Kaduna.

“Duk aikin da ka ba su, za suyi tamkar ni ne nayi, to meyasa zan tsaya ina ta daukar aikin yara, bayan shekaru sun riga sun zo mani?
Shekara ta 62, ta 63 nake nema, Annabi (SAW) a shekara 63 ya bar Duniya. Ka kai wannan, sai ka godewa Allah, ka bar wa wasu su yi.”

Tinubu bai yarda da El-Rufai ba

A ra’ayin Gwamnan, karfinsa ya ragu don haka yake bukatar ya ba yara wuri. Sai dai mutane irinsu Bola Tinubu ba su yarda da hakan ba, yace suna ta gardama a kai.

Hakan martani ne ga masu cewa yana neman kujera, El-Rufai yace wasu na yi masa kazafin da ke rage masa zunubai, a karshe za su yi sanadiyyar shigarsa aljanna.

Kara karanta wannan

An Sha Fama: Bidiyon Yadda Wani Ango Ya Yi Sujjada Tare Da Fashewa Da Kuka A Wajen Daurin Aurensa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng