Ahmad Lawan ya yi Magana Yayin da Jita-jitar Tunbuke shi ke yin Karfi a Majalisa

Ahmad Lawan ya yi Magana Yayin da Jita-jitar Tunbuke shi ke yin Karfi a Majalisa

  • Babu wani Sanata da ya rubuta takarda, yana sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar APC mai mulki
  • Dr. Ahmad Ibrahim Lawan ya tabbatar da wannan a wani jawabi da ya fitar ta bakin Ola Awoniyi
  • Ana cewa Lawan ya ki sanar da sauya-shekar Sanatocin ne saboda tsoron tsige shi daga kujerarsa

Abuja - Ahmad Ibrahim Lawan ya yi watsi da rahotanni da ke cewa wasu Sanatoci sun aiko masa da takardar sauya-sheka daga jam’iyyar APC mai mulki.

Rahoton PM News yace Sanatan Ahmad Ibrahim Lawan ya bada wannan sanarwa ne ta bakin mai taimaka masa wajen harkar yada labarai, Ola Awoniyi.

Mai magana da yawun bakin shugaban majalisar yace labaran da ke yawo duk ba gaskiya ba ne.

Ahmad Ibrahim Lawan ya fitar da jawabin yana mai musanya zargin birne wasikun sauya-shekan wasu Sanatocin APC mai mulki zuwa jam’iyyun hamayya.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Sanatan da APC ke ji dashi a Ribas ya tabbatar da sauya sheka zuwa SDP

Jaridar Blueprint da ta dauko labarin ta rahoto Ahmad Lawan yana mai cewa wasu makiya ne kurum suka kitsa rade-radin domin cin ma burinsu na son rai.

“Mun ga labari a dandalin sada zumunta da wasu jaridun yanar gizo da ke nuna shugaban majalisa, Ahmed Lawan ya birne wasiku daga wasu Sanatoci da ake zargin suna yi masa barazanar sauya-sheka daga jam’iyyar the All Progressives Congress (APC).”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ahmad Lawan
Shugaban Majalisar Dattawa Hoto: @TheSenatePresident / Tope Brown
Asali: Facebook
“Labaran suna nuna Lawan ya birne wasu wasiku domin ya cigaba da zama a kan kujerarsa na shugaban majalisa.”
“Mu na so mu tabbatar da cewa labarin tsantsagwaron karya ne, kuma babu wata wasika a gaban shugaban majalisa.”

Adamu Bulkachuwa ya bar APC?

Rahoton ya ambaci Sanata daya ne kacal, Muhammad Adamu Bulkachuwa a cikin Sanatocin da ake magana a kai.”
“Masu yada wannan karya ba su yi tunanin tantance labarin daga bakin Sanata domin jin ko ya rubuta wata takarda.”

Kara karanta wannan

Jigon Arewa: Babu gwamnatin da talakawa suka sha jar miya kamar ta Buhari

A karshen wasikar, Awoniyi yace Lawan yana karanto wasikar duk wanda ya sauya-sheka domin ya san doka, don haka ne Sanatoci ke kaunarsa.

Angulu da kan zabo

Kun ji cewa Mai neman kujerar ‘Dan Majalisa a Mazabar Ikorodu a Legas ya tuhumi Jam’iyyarsu ta APC da damka tikitin 2023 ga 'Dan Jam’iyyar PDP.

Hon. Oluwatosin Onamade yace Aro Moshood Abiodun da aka tsaida takara, ‘Dan jam’iyyar PDP ne wanda bai da cikakkiyar rajista da APC har yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng