Angulu da kan zabo: Jam’iyyar APC ta ba ‘Dan PDP Takarar Kujerar ‘Dan Majalisa

Angulu da kan zabo: Jam’iyyar APC ta ba ‘Dan PDP Takarar Kujerar ‘Dan Majalisa

  • Ana zargin cewa Aro Moshood Abiodun ba cikakken ‘dan jam’iyyar APC ba ne duk da yana da kati
  • Abokin adawa yace Abiodun ko a kira shi AMA bai yi murabus daga jam’iyyar PDP ba, ya shigo APC
  • A tsakiyar hakan ne Hon Oluwatosin Onamade ya bukaci a ruguza takarar Abiodun a zaben 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagos - Ana zargin jam’iyyar APC da daukar takara, ta ba Aro Moshood Abiodun, wanda ake tunanin shi ba ‘dan jam’iyya mai mulki ba ne.

Bugu da kari, Legit.ng Hausa ta fahimci cewa har ta kai wasu na zargin cewa Aro Moshood Abiodun yana tare ne da jam’iyyar adawa ta PDP.

Aro Moshood Abiodun wanda aka fi sani da AMA shi ne wanda APC ta tsaida a matsayin ‘dan takaran mazabar Ikorodu II a majalisar Legas.

Kara karanta wannan

Ana Tonon Silili, An Fara Fadan ‘Yan APC da Suka Hana Osinbajo Samun Takaran 2023

Idan Aro Abiodun ya yi nasara a zaben 2023, shi ne zai wakilci mutanen yankin Irododu II a majalisar dokokin jihar Legas a karkashin APC.

...Bai da rajista a APC - Hon. Onamade

Wani mai neman zama ‘dan majalisar Ikorodun, Oluwatosin Onamade ya shaidawa Duniya cewa AMA bai da katin zama ‘dan jam’iyya mai-ci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani jawabi da ya fitar, wanda ya shigo hannun Legit.ng, Hon. Onamade yace lambar rajistar Abiodun a matsayin ‘dan APC ita ce 62011.

Aro Moshood Abiodun
Takardar kotu a kan takarar Aro Moshood Abiodun Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Mai harin zama ‘dan majalisar yake cewa ‘dan takaran ya zama ‘dan jam’iyya ne a ranar 29 ga watan Afrilu, mako daya da kammala yin rajista.

Onamade ya hakikance a kan cewa AMA wanda ya yi takara sau uku a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, bai iya sauya-sheka ba har zuwa yanzu.

A dalilin haka ne Onamade ya roki shugabannin APC na jihar Legas da hukumar zabe na kasa watau INEC su ruguza takarar AMA a zaben 2023.

Kara karanta wannan

An Ankarar da Jami’an Tsaro Kan Shirin ‘Yan Ta’adda na Kai Hare-Hare a Legas

Abokin hamayyar ‘dan takarar ya nemi a amince da shi a matsayin wanda ke yi wa APC takara.

Jawabin da Onamade ya fitar

“AMA yana nan a jam’iyyar hamayya ta PDP. Ya yi takara sau uku a jere na neman zama majalisar dokoki na jihar Legas.
Bayan nan sai ya sauya-sheka zuwa APC inda ya shiga takaran Mayun 2022 ta hanyar amfani da katin rajista na karya.
Har yanzu rajistar AMA da PDP tana nan domin bai yi murabus daga jam’iyyar ba.”

Wike da Atiku

Kun samu labari an samu damar zama a jam’iyyar PDP domin a sasanta da Nyesom Wike, amma Wike yace dole ayi waje da shugaban PDP na kasa.

Mutanen Wike sun hadu da Gwamnoni hudu; Seyi Makinde, Okezie Ikpeazu, Samuel Ortom, da Ifeanyi Ugwuanyi da wasu jiga-jigan jam’iyya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng