Gwamna Umahi Na Jihar Ebonyi Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani da Aka Canza

Gwamna Umahi Na Jihar Ebonyi Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani da Aka Canza

  • Gwamnan jihar Ebonyi ya lashe zaɓen fitar da ɗan takarar sanata mai wakiltar mazaɓar kudancin Ebonyi karkashin inuwar APC
  • Magoya bayan APC sun halarci zaɓen wanda ya gudana a hedkwatar ƙaramar hukumar Afikpo ta arewa
  • David Umahi wanda ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na takarar shugaban ƙasa, ya lallasa abokan takararsa da kuri'u 250

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ebonyi - David Umahi, gwamnan jihar Ebonyi, ya samu nasara a zaben fidda gwani na kujerar sanata mai wakiltar mazabar Ebonyi ta kudu da aka canza.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Umahi ya samu kuri'u 250 inda ya lallasa sauran abokan hamayyarsa a karkashin jam'iyyar APC.

An yi zaben a hedkwatar karamar hukumar Afikpo ta arewa inda aka ga cincirindon magoya bayan APC, 'yan jaridu da sauransu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jam'iyyar APC ta lashe zaɓen Ciyamomi 13 da Kansiloli 171 a wannan jihar

Gwamna Dave Umahi.
Gwamna Umahi Na Jihar Ebonyi Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani da Aka Canza Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A yayin bayyana sakamakon, shugaban kwamitin zaben fidda gwanin na kujerar sanatan yankin Ebonyi ta kudu, Farfesa Emmanuel Adebayo ya tabbatar da cewa Umahi ne ya lashe zaben saboda kuri'unsa sun fi yawa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda yace, a cikin jimillar kuri'u 275 da aka kada, 268 ne masu amfani yayin da aka yi asarar 7.

Punch ta ruwaito Ya ce:

"Austin Chukwu Umahi ya samu kuri'u 10; Ann Agom Eze ya samu 0; David Umahi ya samu kuri'u 250; Ibiam Margaret ta samu kuri'u 3; Chukwu Elizabeth Nwakaego ta samu kuri'u 5."
"Da karfin ikon da aka bani, na bayyana Umahi a matsayin wanda ya ci zaben nan sakamakon kuri'u 250 da ya samu."

Kun min kara - Gwamna Umahi

A jawabinsa, Gwamna Umahi ya mika godiyarsa ga magoya bayansa kan karar da suka masa kuma ya kwatanta tikitinsa a matsayin mai karfi sosai.

Kara karanta wannan

Ka fi su gaskiya dattijo, mutuwa ce kadai zata raba mu, Matashi ya jaddada kaunarsa ga Buhari

"Tikitin mai karfi ne. Ina mika godiya gareku kan karar da kuka yi min. Na karba wannan karamcin da Ubangiji yayi min. Na yi gwagwarmaya a dukkan rayuwata kuma duk na cinye su."

- Umahi

A wani labarin kuma Na Kusa Da Gwamna Tambuwal Da Kansiloli Takwas Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC

Makusancin Gwamnan jihar Sokoto kuma shugaban karamar hukumar Tangaza, Isah Bashar Kalanjine, ya bar jam'iyyar PDP zuwa APC.

Makusancin Gwamna Tambuwal din ya kara da yin tsarabar kansilolin karamar hukumarsa takwas zuwa jam'iyya mai mulkin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262