Ka fi su gaskiya dattijo, mutuwa ce kadai zata raba mu, Matashi ya jaddada kaunarsa ga Buhari

Ka fi su gaskiya dattijo, mutuwa ce kadai zata raba mu, Matashi ya jaddada kaunarsa ga Buhari

  • Fitaccen masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sirajo Saidu Sokoto, ya sake jaddada kaunarsa ga shugaban kasan
  • A wallafar da yayi a Facebook, ya sanar da cewa dattijon shugaban kasan yafi masu zaginsa gaskiya kuma mutuwa ce kadai ce zata raba su
  • Sanannen masoyin shugaban kasan ya saba caccakar masu sukar Buhari duk da sace 'yan uwansa maza 5 da 'yan bindiga suka yi a Sokoto shekarar da ta gabata

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani 'dan gani-kashenin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa mutuwa ce kadai za ta raba shi da shugaban kasan.

Idan za mu tuna, Sirajo Saidu Sokoto a shekaar da ta gabata ya yi bore tare da sanar da cewa baya tare da shugaban kasan bayan 'yan bindiga sun yi awon gaba da 'yan uwansa maza har biyar a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Gwmnatin Tarayya Ta Saya Wa Jamhuriyyar Niger Motocin Naira Biliyan 1.4

Sirajo Saidu Sokoto
Ka fi su gaskiya dattijo, mutuwa ce kadai zata raba mu, Matashi ya jaddada kaunarsa ga Buhari. Hoto daga Sirajo Saidu Sokoto
Asali: Facebook

Saidu fitaccen masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook kuma an san ya kware wurin caccakar masu zukar shugaba Buhari da jam'iyyar APC.

A ranar Juma'a, 29 ga watan Yulin 2022, ya sake jaddada goyon bayansa da kauna ga shugaban kasan Muhammadu Buhari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ka fi masu zaginka gaskiya dattijo. Mun yi alkawarin mutuwa ce kadai zata raba mu da Buhari," ya rubuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel