Gwamna Tambuwal Ya Karbi Wani Babban Jigon APC Da Ya Koma PDP
- Gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal ya karbi wani babban jigon APC a jihar da ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP
- Ɗahiru Yabo wanda ya samu kyayyawan maraba, ya ce ba zai iya zama cikin tawagar da ba ta da demokaraɗiyya a cikin gida
- Zaɓen 2023 na ƙara matsoawa kowace jam'iyyar siyasa na kokarin shirya wa domin ganin ta cimma nasara
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Sokoto - Gwamnan Sakkawato, Aminu Waziri Tambuwal, ya tarbi wani babban jigon APC reshen jihar, Ɗahiru Yabo, zuwa jam'iyyar PDP.
Jaridar Punch ta tattaro cewa Yabo ya rike muƙamin kwamishinan yaɗa labarai da kwamishinan albarkatun ƙasa a baya.
Tsohon jigon APC ya samu tarba ta musamman daga gwamna Aminu Tanbuwal, mataimakin gwamana, Mannir Muhammad Iya, da Sakataren gwmanatin Sakkawato, Muhammad Ahmad.
Haka nan shugaban PDP a jihar Sakkwato, Alhaji Bello Muhammad da wasu manyan jami'an gwamnati sun samu halartar taron karɓan jigon jam'iyyar adawa a jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Meyasa ya sauya sheƙa?
A wata sanarwa da mai baiwa gwamna Shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Muhammad Bello, ya fitar, ta nuna cewa Yabo ya sauƙa sheƙa ne saboda rashin adalcin cikin gida a APC, da yawan alfarma.
Da yake jawabi, Yabo ya ce:
"Jam'iyyar PDP a jihar Sakkwato ta gina wata gwamnati ne da tilas ka zama mamba idan har kana so a tafi dakai ko kuma kana son kawo cigaba a ƙasa baki ɗaya ko kuma jiha."
"Da izinin Allah, zamu goyi bayan tawagar gwamna Aminu Waziri Sakkwato, ɗan takarar gwamna karkashin inuwar PDP a jihar da sauran yan takara da jam'iyya ta tsayar a wasu kujerun."
A wani labarin kuma batun tsige shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya girmama, Sanatocin APC na cigbaa da goyon baya
Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazaɓar Adamawa ta arewa, Sanata Elisha Abbo, ya goyi bayan a tsige shugaba Buhari.
A wani taron mambobin APC kiristoci da ya gudana a Abuja, Sanatan ya bayyana cewa Buhari ya gaza sauke babban nauyin dake kansa.
Asali: Legit.ng