Rabiu Kwankwaso ya taya Daniel Okon Murnar Zama sabon shugaban kungiyar CAN

Rabiu Kwankwaso ya taya Daniel Okon Murnar Zama sabon shugaban kungiyar CAN

  • Rabiu Kwankwaso ya taya Rabaren Fada Okon Murna zama sabon shugaban kungiyar Kristocin Najeriya CAN
  • Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso ya ce sabon shugaban kungiyar CAN NE mutum mai kishin kasar sa
  • A ranar Litinin na ne Kungiyar Kristocin Najeriya CAN ta zabi Daniel Okon a matsayin sabon shugaban ta

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, Rabi'u Kwankwaso, ya taya Mai Alfarma Daniel Okoh Murna zama sabon shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN. Rahoton PUNCH

Tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana Ravaren Daniel Okon a matsayin mutum mai kishin kasa kuma gwarzo a wajen tattaunawar zaman lafiya a tsakanin addinai wato Inter Faith.

Kwankwaso ya ce, Najerya za ta ta yi kyau idan dukkanin mallam addini za su aiki da hakuri da juriya.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ko Tinubu? Afenifere Ta Bayyana Dan Takarar Shugaban Kasa Da Za Ta Goyi Baya a 2023, Ta Bada Dalili

KWANWASO
Rabiu Kwankwaso ya taya Daniel Okon Murnar Zama sabon shugaban kungiyar CAN FOTO VANGUARD
Asali: Facebook

Kwankwaso ya bayyana haka ne a sakon taya murna ga Raveren Daneil Okoh, wanda ‘yan jarida suka samu a Abuja ranar Asabar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An zabi Rev. Okoh ne a ranar Litinin domin ya gaji Rev. Samson Olusupo Ayokunle, bayan ya kammala wa’adinsa a matsayin shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya CAN.

Mambobin APC ne kan gaba wajen neman tsige Buhari, in ji Shekarau

A wani labari kuma, Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau,yace mambobin jam’iyyar APC suka soma gabatar da yunkurin Tsige shugaba Buhari daga karagar mulkin kasar. Rahoton BBC

Sun gabatar da kudurin tsige shugaba Buhari da sharadin ya gaggauta daukar mataki akan tabarbarewar tsaro a kasar ko su yi waje dashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa