Rabiu Kwankwaso Ya Gargadi ’Yan Majalisa Kan Tsige Buhari

Rabiu Kwankwaso Ya Gargadi ’Yan Majalisa Kan Tsige Buhari

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya gargadi yan Majalisar Najeriya da su yi hattara da yunkurin tsige Buhari kan matsalar tsaro
  • Dakta Rabiu Kwankwaso ya ziyarci jihar Kwara dan kaddamar ofishin jam’iyyar NNPP a birnin Ilorin
  • Gwamna Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq, ya shawarci ’yan siyasa da su guji siyasar gaba a lokacin da yake karbar bakuncin Kwankwaso

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kano - Rabiu Musa Kwankwaso ya ja kunnen ’yan Majalisar Najeriya da su bi a hankali kan yunkurin tsige SBuhari da suke kokarin yi kan Matsalar tsaron Najeriya. Rahoton Aminiy.Daily.Trust

Kwankwaso wanda tsohon Ministan Tsaro ne ya gargadi ’yan Majalisar cewa kokarin tsige Buhari abu ne da zai iya tada tarzoma a Najeriya.

Tsohon Ministan, ya ce tabbas al’amarin tsaro a Najeriya ya lalace kuma ya kamata gwamnati ta zage dantse wajen ganin an kawo karshen matsalar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Goyi Bayan A Tsige Buhari

Buhari
Rabiu Kwankwaso Ya Gargadi ’Yan Majalisa Kan Tsige Buhari FOTO Legit.NG
Asali: Depositphotos

Kwankwaso wanda ke takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria Party NNPP ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, dan halartar taron bude da ofishin jam’iyyar NNPP a birnin Ilorin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamna Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq, ya shawarci ’yan siyasa da su guji siyasar gaba a lokacin da yake karbar bakuncin Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.

A ranar Juma’a 29 ga watan Yuni 2022 Kwankwaso ya kai ziyarar ban girma ga Mai Martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari.

An Baiwa Jami’in Karotan Da Ya Kama Manyan Motocin Giya, Tukuicin Naira Miliyan 1

A wani labari kuma, Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta baiwa daya daga cikin jami’anta Halilu Jalo kyautar Naira miliyan 1 bisa kama wasu manyan motoci guda biyu da giya a jihar. Rahoton Premium Times

Mista Jalo ya ki karbar cin hancin Naira 500,000 da aka ce mai barasa ya ba shi domin a sako motocin da aka kwace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa