Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Goyi Bayan A Tsige Buhari
- Gwamna Samuel Ortom ya goyi bayan yunkurin tsige Shugaba Muhammadu Buhari da majalisa ta yi
- A cewar gwamnan na Jihar Benue, ba zai yiwu a kyalle kasar ta cigaba da rashin kwarewa ba
- Ya bayyana cewa akwai babban bukatar a farfado da tattalin arzikin tsaron Najeriya
FCT, Abuja - Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue ya goyi bayan yunkurin da majalisar dattawa na tsige Shugaba Muhammadu Buhari saboda matsalar tsaro da ke adabar kasar.
A cewar wani rahoto da jaridar ThisDay ta fitar, Gwamna Ortom na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya jinajinawa majalisar tarayyar kan wa'adin sati-shida da ta bawa shugaban kasa.
Legit.ng tunda farko ta rahoto cewa sanatocin jam'iyyun hamayya karkashin jagorancin Sanata Philip Aduda na Abuja, cikin fushi sun fita daga zauren majalisar bayan Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya ki sauraron kudin tsige Shugaba Muhammadu Buhari.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamna Ortom ya bayyana goyon bayansan ne a masaukinsa da ke Abuja, ranar Juma'a 29 ga watan Yuli yayin tarbar tawagar yan majalisa marasa rinjaye da Sanata Philip Aduda ya yi wa jagoranci.
Gwamna Ortom ya jinjinawa jarumtar yan majalisar
Yayin da ya ke magana da tawagar, Gwamna Ortom jarumtarsu da kishin kasa ya birge shi ya kuma mika godiyarsa ga wasu sanatocin jam'iyyar APC da suka goyi bayan tsige Buhari.
Gwamna Ortom ya bayyana cewa Shugaba Buhari bai tabuka wani abin a-zo-a gani ba kuma ya gaza wurin samar da tsaro da inganta tattalin arziki da ma wasu bangarorin.
A bangarensa, Sanata Aduda wanda ya jagoranci tawagar ya fadawa Ortom cewa sun taho su masa jawabi kan lamarin ne kasancewarsa daya daga cikin masu karfin iko a PDP.
Aduda ya fada wa gwamnan duk da sanatoci suka fara yunkurin, yan majalisar wakilai da wasu yan APC sun goyi baya.
Sanata Orker Jev da Hon Samson Okwu suna cikin wadanda suka tafi ziyarar.
Sanata Daga Arewa Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Baya Goyon Bayan Tsige Buhari
A wani rahoton, shugaban kwamitin labarai da wayar da kan kasa na majalisar dattawa, Danladi Sankara ya nesanta kansa daga shirin da ake yi na tsige Shugaba Muhammadu Buhari, rahoton Daily Trust.
Sanata Sankara, wanda ke wakiltar Jigawa North West a Majalisar ya kuma nesanta kansa daga shirin tsige shugaban majalisa, Ahmad Lawan.
Sanatocin jam'iyyun adawa, a ranar Laraba, bayan tattaunawa na away biyu sun bawa Buhari wa'adin wata shida ya magance matsalar tsaro ko kuma su tsige shi.
Asali: Legit.ng