Zan Kawo Karshen Yan Bindiga A Zamfara Idan Na Zama Shugaban ƙasa, Atiku
- Atiku Abubakar ya kai ziyara jihar Zamfara, ya sha alwashin dawo da zaman lafiya idan ya ɗare kujerar shugaban ƙasa
- Ɗan takarar, wanda ya karɓi jiga-jigan APC da suka sauya sheka zuwa PDP, ya ce abu na farko da za'a fara yi shi ne kawar da APC daga mulki
- Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da ayyukan ta'addancin yan bindiga ya fi ƙamari a arewa maso yamma
Zamfara - Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sha alwashin ceto jihar Zamfara daga hannun yan ta'adda, waɗan da suka kashe, garkuwa da raba dubbanin mutane da gidajen su, idan ya zama shugaban kasa.
Atiku ya ɗauki wannan alƙawarin ranar Laraba da daddare bayan gana wa da ɗan takarar gwamnan Zamfara karkashin PDP, Dauda Lawal Dare.
Jaridar Premium Times ta ruwaito Atiku Abubakar na cewa mutanen Zamfara na gab da tsira daga halin da suka tsinci kan su.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya zargi jam'iyyar APC mai mulki da sakaci har matsalar ta yaɗu, yanayin da a cewarsa ya maida jihar koma baya da talakawanta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A wata sanarwa da hadimin ɗan takarar gwamnan Zamfara ya fitar, Atiku ya ce matakin farko na ceto jihar shi ne mutane su maka APC da ƙasa a zaɓe.
Atiku ya ce:
"Idan muna son cimma nasara dole mu haɗa kai a PDP hakan zai bamu cikakken damar fuskantar abokan hamayya duk rintsi duk wuya."
"Babban abinda mazauna Zamfara ke so a musu shi ne a dawo da zaman lafiya, a tsare gonaki da kuma samar da kasuwanci. Amma yanayin yanzu ba haka yake ba, wajibi mu kawar da PDP don ceto da gina jiha da kasa baki ɗaya."
2023: Rikicin PDP Ya Dauki Sabon Salo, Gwamnoni Da Ke Goyon Bayan Wike Sun Gindayawa Atiku Sabbin Sharruda Kafin Su Mara Masa Baya
Jiga-Jigan APC sun koma PDP
Yayim ziyarar Atiku ya karɓi tsofaffin jiga-jigan jam'iyyar APC, waɗan da suka sauya sheƙa zuwa PDP a jihar Zamfara.
Mista Lawal Dare ya ce masu sauya shekan sun gaji da karerayin da ake musu a APC yasa suka yanke haɗa kai da tawagar jam'iyya mai nasara.
Legit.ng Hausa ta tattaro wasu daga cikin waɗan da suka sauya sheƙa, sun haɗa da, Salihu Mai Buhu, Sahabi Liman, Illili Bakura, Garba Yandi, Ikra Bilbis, Na’Allah Isa Mayana, Mukhtar Lugga, da sauran su.
A wani labarin kuma Ɗan Takarar Shugaban Kasa Na ADC, Kachikwu, Ya Bayyana Buhari A Matsayin Mataimakinsa
Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar ADC, Dumebi Kachikwu, ya bayyana Ahmed Buhari a matsayin abokin takararsa.
Da yake tsokaci kan halin da ƙasa ke ciki, Kachikwu ya ce idan ADC ta kafa gwamnati zata dawo da zaman lafiya.
Asali: Legit.ng