Gwamnatin Buhari ta yi martani kan barazanar da Sanatocin PDP suka yi na tsige Buhari saboda rashin tsaro
- Fadar shugaban kasa ta yi martani ga batun da sanatoci suka dauko na cewa za su tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Lamurran tsaro suna kara ta'azzara a Najeriya, 'yan bindiga sun fara shiga yankunan da ba a yi tsammani ba a kasar
- A baya 'yan bindiga sun yi barazanar sace shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru El-Rufai
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta mayar da martani kan barazanar da Sanatocin jam’iyyar PDP suka yi na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari, The Cable ta ruwaito.
A ranar Laraba ne ‘yan majalisar suka baiwa shugaban kasar wa’adin makwanni shida domin ya magance matsalar rashin tsaro ko kuma ya fuskanci batun tsige shi.
Da yake magana bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), Lai Mohammed, ministan yada labarai, ya ce gwamnatin tarayya tana aiki ba dare ba rana don ganin ta magance matsalolin tsaro.
Da yake amsa tambayoyin 'yan jarida da kuma karin haske ga batun tsige Buhari, ministan ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ina so in tabbatar muku cewa shugaban kasa yana sane da wadannan abubuwa duka, kuma a hakikanin gaskiya, ina ganin gobe, za a sake yin wani taron majalisar tsaro.
“Saboda haka, ba batu ne da shugaban kasa ya dauka da wasa ba, kuma kamar yadda a ko da yaushe nake fadi, wasu matakan da za mu dauka ba matakan da za mu tattauna a fili ba ne a nan. Amma mun damu kamar yadda kuka damu. Ba za mu yi watsi da hakkinmu ba."
Yada farfaganda suke kawai, kuma abin dariya ne
Da yake yawabi game da barazanar 'yan bindiga na cewa za su sace shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Kaduna Mallam Nasiru El-Rufai, ministan ya ce ‘yan ta’addan suna kawai yada farfaganda ne.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, ministan ya ce batun sace Buhari batu ne na ban dariya wanda ba ma zai yiwu ba.
A kalamansa:
"Muna yin duk mai yiwuwa don ganin cewa daukacin al'ummar kasar na cikin kwanciyar hankali kuma lokaci ya yi da za a ga sakamako. Dangane da wadanda suka yi barazana ga shugaban kasa, ina ganin ya fi kama da farfaganda fiye da komai. Abin dariya ne."
Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Sace Buhari Da El-Rufai A Sabon Bidiyo
A wani labarin, yan makonni bayuan farmakin da aka kaiwa ayarin motocin shugaba Muhammadu Buhari a jihar Katsina, yan ta’adda sun yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasar na Najeriya.
An dai farmaki tawagar tsaron shugaban kasar a hanyarsu ta zuwa mahaifar Buhari da ke Daura gabannin bikin Sallah. Mutane biyu sun jikkata a harin wanda aka ce fadar shugaban kasar ta dakile.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, a cikin sabon bidiyon da suka saki, yan bindigar wadanda suka sace fiye da fasinjoji 60 a jirgin kasar Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, sun yi barazanar sacewa da kuma halaka Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
Asali: Legit.ng