Jam'iyyar APC Ta Bayyana Sanata Gobir A Matsayin Sabon Shugaba A Majalisar Dattawa

Jam'iyyar APC Ta Bayyana Sanata Gobir A Matsayin Sabon Shugaba A Majalisar Dattawa

  • Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta zaɓi Sanata Gobir daga jihar Sakkawato a matsayin sabon jagoran majalisar dattawa
  • Sanata Abdullahi Adamu, shugaban aPC na ƙasa ne a sanar da haka a wata takarda da ya aike wa majalisar ranar Laraba
  • Gobir zai maye gurbin Sanata Yahaya Abdullahi, wanda ya yi murabus daga muƙamin bayan ya sauya sheƙa

Abuja - Jam'iyyar All Progressive Congress watau APC ta ayyana sunan ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Sokoto ta gabas, Sanata Abdullahi Gobir, a matsayin jagoran masu rinjaye na majalisar Dattijai.

Wannan na ƙunshe ne a wata wasiƙa da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya aike wa majalisar Datttawa kuma shugaban majalisa, Sanata Ahmad Lawan ya karanta da zaman yau Laraba.

Sanata Abdullahi Gobir.
Jam'iyyar APC Ta Bayyana Sanata Gobir A Matsayin Sabon Shugaba A Majalisar Dattawa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sanata Gobir zai maye gurbin Sanata Yahaya Abdullahi (Mai wakiltar Kebbi ta arewa) biyo bayan murabus ɗin da ya yi daga mukamin jagoran majalisa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana Batun Tsige Shi, Shugaba Buhari Ya Naɗa Surukinsa Da Wasu Mutum Biyu Manyan Muƙamai A Tarayya

Sanatan ya yi murabus daga muƙamin ne bayan ya ɗauki matakin sauya sheka daga APC mai mulki zuwa babbar jam'iyyar hamayya watau PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wasikar APC, Abdullahi Adamu, ya bukaci Sanata Gobir ya maye gurbin Sanata Yahaya Abdullahi wanda ya sauya sheka a watan Yuni, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Meyasa Sanatan ya bar APC?

Tsohon jagoran majalisar dattawan ya ce ya zaɓi ya koma tsagin hamayya ne domin ya haɗa karfi da ƙarfe da masu yaƙi da rashin iya mulki, ƙaƙaba mutane da saɓa wa tsarin demokaraɗiyya.

Ya ce ƙalubalen da matsalolin da suka hana APC a jihar Kebbi sakat, sun fara ne a ɓara, "lokacin da gwamna ya fara girbe jagorancin jam'iyya ta jiha, yana ƙaƙaba mutane a shugaban gunduma, ƙananan hukumomin da matakin jiha."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sanatoci sun yi barazanar tsige shugaba Buhari, sun ba shi wa'adin mako 6

"Sabida haka, bayan na gaza samun adalci a tsohuwar jam'iyya ta APC, na tsallake zuwa PDP tare da dumbin magoya baya na." inji Sanatan.

A wani labarin kuma Bidiyon Hatsaniyar da ta auku a majalisar Dattawan Najeriya kan bukatar tsige Buhari

Sanatocin jam'iyyun hamayya sun fice daga zauren majalisar Dattawa biyo bayan kira a tsige shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari daga kujerarsa.

Channels TV ta ruwaito cewa hakan ya biyo bayan wata Dirama da ta auku a zaman mambobin majalisar Dattaawa ta ƙasa yau Laraba a Abuja, babban birnin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262