2023: Kwankwaso Da Peter Obi Duk 'Yan Kallo Ne, Zabe Tsakanin Tinubu Da Atiku Ne, Gwamna Sule

2023: Kwankwaso Da Peter Obi Duk 'Yan Kallo Ne, Zabe Tsakanin Tinubu Da Atiku Ne, Gwamna Sule

  • Injiniya Abdullahi Sule, gwamnan Jihar Nasarawa ya ce zaben shugabancin kasa na 2023 tsakanin Tinubu da Atiku ne
  • Gwamna Sule ya ce bisa ga dukkan alamu Peter Obi na LP da Rabiu Kwankwaso na NNPP ba za su kai labari ba don magoya bayansu a wani bangaren kasa kawai suke
  • Sule ya ce galibin mutanen jiharsa ba su san wanene Obi ba, kuma da NNPP da LP sun yi maja da watakila su tabuka wani abu amma da wuya su ci zabe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce zaben shugabancin kasa na 2023 tsakanin jam'iyyar APC da PDP ne, rahoton Channels Television.

Da ya ke watsi da yiwuwar nasarar dan takarar Labour Party, Peter Obi da New Nigerian Peoples Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso, Sule ya ce sun rasa damarsu na zama cikin karfi a zaben tunda suka gaza hada kai.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Matashi ya fitar da bidiyo yana barazanar harbe duk wanda ya zabi Atiku ko Tinubu

Gwamna Abdullahi Sule.
Babu Wanda Ya San Peter Obi a Jihar Nasarawa, Zaben 2023 Tsakanin Tinubu Da Atiku Ne, Gwamna Sule. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hirar da aka yi da shi a Channels Television a ranar Litinin 25 ga watan Yuli, gwamnan ya ce yan takarar jam'iyyun biyu ba su da magoya baya a sassan Najeriya da za su iya cin zaben shugaban kasa.

Ya ce:

"Ba a ma san shi sosai a Jihar Nasarawa ba, don haka ban san a kasa ba. A matakin kasa, bisa abin da muke karantawa, akwai jam'iyyu hudu masu karfi, APC saboda mune ke mulki da PDP don tana da dan takara nagartacce.
"Peter Obi ya taba yin gwamna don haka yana nan tare da jam'iyyar Kwankwaso.
"Idan ka dubi yan takarar nan, idan za ka yi adalci, yan takara biyu ne kawai ke sama kuma sune Asiwaju da Atiku Abubakar."

Da ya ke jadada cewa ba yana watsi da Obi da Kwankwaso bane, Sule, ya ce zai musu wahala su ci zabe.

Kara karanta wannan

An kai wa 'Dan Majalisar Daura, 'Danuwan Shugaba Buhari Hari Har Gida a Katsina

Sule ya ce hanya guda da ya dace su yi babban tasiri shine su yi maja tunda farko.

2023: Awanni Bayan Kaddamar Da Abokin Takarar Kwankwaso, Wasu Jami'an NNPP Sun Riga Mu Gidan Gaskiya

A bangare guda, rahotanni sun bayyana cewa a kalla jami'an jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) guda hudu ne suka mutu a jihar Neja sakamakon hatsarin mota.

Shugaban NNPP na Jihar, Mamman Damisa, ya shaida wa yan jarida a ranar Lahadi, ranar 24 ga watan Yuli, cewa lamarin ya faru a kan hanyar Lambata/Bida a yayin da jiga-jigan jam'iyyar da jam'ianta ke dawowa daga tafiya da suka yi bayan kaddamar da mataimakin Rabiu Musa Kwankwaso.

A cewar Damisa, shugabannin jam'iyyar na kananan hukumomi biyu, shugaban matasan jam'iyyar daya da direba sun mutu a hatsarin, The Punch ta rahoto.

Martanin Wasu Magoya Bayan Peter Obi a Jihar Nasarawa

Legit Hausa ta samu ji ta bakin wasu matasa magoya bayan Mr Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP don jin martaninsu game da kalamen Gwamna Sule.

Kara karanta wannan

Amaechi: Daliget Da Suka Sayar Da Kuri'unsu Yayin Zaben Fidda Gwani Na APC Suna Nadama

David Ose, matashi ne wanda ya ce yana sa'ar dinki kuma mazaunin Jihar Nasarawa ya ce abin da Gwamna Sule ya fada karya ne tsantsagwaronta da farfaganda na siyasa.

Ya kuma ce yana goyon bayan Obi ne saboda ayyuka da ya yi a baya lokacin da ya ke gwamna da kuma cancanta duk da shi dan arewa ne kuma ba ibo ba.

"Na yi imanin zai iya kawo gyara ga halin da muke a Najeriya yanzu, muna shirin yin tarurruka a Lafia da Akwanga da wasu wurarre da za su girgirza mutane.
"Muna kan shirye shiryen yanzu amma dai ba a tsayar da rana ba, idan an tsayar za mu sanar da ku," in ji shi.

Hazalika, shima wani matashi Saeed Ogba, mazaunin Nasarawa ya ce kalaman gwamnan ba gaskiya bane.

Obi yana ga magoya baya sosai musamman cikin matasa kuma idan lokacin zabe ya yi za su fito su kada kuri'ansu ga dan takarar na LP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164