Rigingimu Sun Nutsar da Jam’iyya, INEC ta Fitar da ‘Yan takara Babu APC a 2023
- Hukumar INEC ta fitar da jerin wadanda za su shiga zaben Gwamnan jihar Akwa Ibom a 2023
- Rahotanni sun tabbatar da cewa jam’iyyar APC ba ta da ‘dan takaran Gwamna a jihar a zaben badi
- Jam’iyyar ta samu kanta ne a cikin wasu rigingimun cikin gida da ya shafi zaben fitar da gwani
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Akwa Ibom - Jam’iyyar APC mai rike da mulkin Najeriya ba ta da ‘dan takarar kujerar Gwamna daga jihar Akwa Ibom a zabe mai zuwa na shekarar 2023.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa daga cikin jerin ‘yan takaran da hukumar INEC ta fitar a Akwa Ibom, ba a ga sunan wanda zai tsayawa APC takara ba.
Da aka zo kan sunan ‘dan takaran jam’iyyar APC na kujerar Gwamna, sai aka bar wurin wayam. Sauran jam'iyyu duk su na da 'yan takararsu a 2023.
Premium Times tace hukumar zabe na kasa watau INEC ta fitar da sunayen wadanda za su shiga zabe ne a wata takarda da aka fitar a hedikwata a Uyo.
A karshen makon jiya aka saki sunayen ‘yan takaran gwamnan, aka tabbatar da cewa ba a tsaida wanda zai rikewa APC tuta a jihar Akwa Ibom ba.
Akan Udofia ya fice daga APC
Akan Udofia shi ne ake ikirarin ya lashe zaben zama ‘dan takaran APC a jihar, amma hukumar INEC tace ba ta san da zaben fitar da gwanin da aka yi ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ana haka sai aka ji labarin Akan Udofia ya sauya-shekarsa daga APC zuwa jam’iyyar PDP.
APC ta hadu da dokar zabe
Duk zaben fitar da gwanin da jami’an INEC ba su samu halarta ba, tamkar yake da babu a sabuwar dokar zaben da Muhammadu Buhari ya sa wa hannu.
Kwamishinan zabe na Akwa Ibom, Mike Igini ya gabatarwa INEC rahoto a ranar 27 ga watan Mayu, yana sanar da cewa APC ba ta tsaida ‘dan takara ba.
Har zuwa yanzu matsayin hukumar zaben shi ne ba ta gudanar da zaben fitar da gwani a jam’iyyar APC ba, abin da hakan ke nufi shi ne ta rasa takara.
Rikicin APC na cikin gida a jihar ya jawo jami’an INEC suka kai har karfe 10:30 na dare a filin Sheergrace Arena a ranar, amma ba a fara zaben gwani ba.
Bassey Albert ya bar PDP
Kwanakin baya an ji labari Sanata Bassey Albert, ya fice daga jam'iyyar PDP a Akwa Ibom. Daga baya Albert ya bada sanarwar komawarsa jam'iyyar YPP.
Guguwar sauya sheka ta sake shiga majalisar dattawan Najeriya, Sanatan wanda ya yi shekara bakwai yana Kwamishina Akwa Ibom ya hakura da PDP.
Asali: Legit.ng