Peter Obi ya maida wa Atiku martani, ya ce abun Al'ajabi zai faru a 2023

Peter Obi ya maida wa Atiku martani, ya ce abun Al'ajabi zai faru a 2023

  • Tsohon gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa ya ce ya ƙosa ya ba da mamaki a babban zaɓen 2023
  • Peter Obi, yayin martani ga kalaman Atiku Abubakar na PDP, ya ce dama can rayuwar siyasarsa cike take da abubuwan Al'ajabi
  • A kwanakin nan dai yan takarar shugaban kasa na ta musayar yawu kan abubuwan daban-daban

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya ce ya ƙagara ya shaida Al'ajabin samun nasararsa a babban zaɓen 2023, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Obi ya yi wannan furucin ne a wata hira da gidan Talabijin na Channels TV ranar Litinin, 25 ga watan Yuli, 2022.

A ranar 22 ga watan Yuli, Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, ya bayyana cewa tsammanin Obi zai iya lashe zaɓen kansa wani, 'Abun al'ajabi' ne.

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gida: Gwamnan PDP ya maida wa Atiku martani kan kalamansa na zaɓen mataimaki

Peter Obi.
Peter Obi ya maida wa Atiku martani, ya ce abun Al'ajabi zai faru a 2023 Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

"Da wahala ka yi tsammanin abun Al'ajabi zai faru kawai saboda Peter Obi ya shiga jam'iyyar Labour Party. Duk bayan haka suna da ɓaɓatu a kafafen sada zumunta," a cewar Atiku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin Obi ga Atiku

Da yake martani ga tsohon mataimakin shugaban kasan, Obi ya ce tun da ya tsoma hannu a siyasa, baki ɗaya harkokinsa cike suke da abubuwan Al'ajabi.

"Al'ajabi shi ne tushen imanin mu kuma shi yake ƙara mana karfin imani. A wurina tun da na shiga siyasa, nasarori na da tarihin da na kafa duk sun kasance abun Al'ajabi."
"Duk abubuwan da suka faru suna da ban Al'ajabi, idan kuka duba na nemi gwamna a jam'iyyar da bata kai shekara ɗaya ba a 2003, na lashe zaɓe, suka ayyana wani daban, na tafi Kotu."
"Kowa na cewa ba zai yuwu ba, ba hanya kuma ba'a taɓa haka ba a baya, bayan shekara uku Kotu ta ayyani wanda ya yi nasara, na karɓi shahadar aiki."

Kara karanta wannan

2023: Atiku, Tinubu sun gamu da cikas a kokarin gaje Buhari, wasu ɗaruruwan mambobin PDP da APC sun sauya sheƙa

Obi ya kara da cewa watanni 6 bayan haka aka tsige shi daga kujera tare da wasu gwamnoni biyu, "Na koma Kotu, ni ne gwamna na farko da na koma kan kujerata."

A wani labarin kuma Mambobi 20,000 sun sauya sheƙa zuwa APC a jiha ɗaya, Shugabar mata ta rungume su hannu biyu

Shugabar matan APC ta ƙasa, Dakta Betta Enu, ta karɓi dubbannin masu sauya sheƙa zuwa APC a mahaifarta da ke jihar Kuros Riba.

A wani taro da aka shirya domin tarbar mutanen, Enu ta tabbatar musu da cewa ba za'a nuna musu banbanci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262