Shugaban kasa ya Bada Sabon Mukami, ya Maye Gurbin Wanda ya ba Minista a Kano
- Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi sabon mai ba shi shawara kan harkokin majalisar tarayya
- Nasiru Babale Illa zai rika taimakawa Shugaban Najeriya a kan duk sha’anin ‘yan majalisar wakilai
- Hon. Illa ya gaji kujerar da su Umar El-Yakub da kuma Abdulrahman Kawu Sumaila suka rike a baya
Abuja - Mai girma Muhammadu Buhari ya amince da nadin Nasiru Babale Illa a matsayin babban mai bada shawara kan harkokin da suka shafi majalisa.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya sanar da wannan mukami da aka bada a wani jawabi na musamman da ya fitar a yammacin Lahadi.
Malam Garba Shehu ya ce Honarabul Nasiru Babale Illa zai rika taimakawa Muhammadu Buhari a kan sha’anin ‘yan majalisar wakilan tarayya a kasa.
The Guardian ta ce Nasiru Baballe Illa ya yi karatunsa ne a makarantu irinsu Victory College, Alexandria, da kuma West London College da ke kasar Birtaniya.
Tun 2015 ya rasa kujerarsa
Illa ‘dan kasuwa ne wanda ya kware wajen harkar rini, jima da sauransu, kafin ya shiga siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehu yake cewa wanda aka ba mukamin yana cikin ‘yan kungiyar Akantoci na Najeriya watau ANAN, ya canji Hon. Umar El-Yakub da ya zama Minista.
Hon. Illa ya wakilci mazabar Tarauni a majalisar wakilan tarayya tsakanin shekarar 2011 da 2015. Daga baya ya rasa tikitin APC a hannun Hon. Hafizu Kawu.
Hon. Hafizu Kawu hadimi ne a ofishin shugaban kasa a lokacin, ya kasance cikin manyan masu ba mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo shawara.
Kujerar SSA ta ki barin Kano
Idan za a tuna, shi ma Umar El-Yakub wanda aka ba kujerar Minista a madadin Sabo Nanono, tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayya ne daga jihar Kano.
Kafin El-Yakub, wanda ya rike wannan matsayi na Hadimin shugaban kasa shi ne Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila, shi kuma ya ajiye aikinsa a 2019.
Sanusi II ya yi tir
A makon jiya aka ji labari Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) ta shirya wani taro ta yanar gizo wanda Muhammadu Sanusi II ya yi jawabi.
Khalifa Muhammadu Sanusi yana ganin har gobe akwai gyara a dokar zaben kasar nan, domin ana amfani da kudi wajen sayen zabin al’umma a Najeriya.
Asali: Legit.ng