Atiku Tantirin Maƙaryaci Ne, In Ji Tinubu, Ya Tona Abin Da Ya Faru Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi a 2007

Atiku Tantirin Maƙaryaci Ne, In Ji Tinubu, Ya Tona Abin Da Ya Faru Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi a 2007

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kira takwararsa na PDP, Atiku Abubakar makaryaci
  • Tinubu yana martani ne kan ikirarin da Atiku ya yi na cewa ya ki amincewa da shi Tinubun a matsayin abokin takara a 2007 saboda gujewa tikitin musulmi da musulmi
  • Dan takarar na shugaban kasar APC ya ce ikirarin na Atiku karya ne, ya kara da cewa dan takarar na PDPn ne ya yi masa tayin tikitin takarar na mataimaki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, a ranar Juma'a ya ce Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP 'tantirin' maƙaryaci ne, rahoton The Cable.

Tinubu ya furta hakan ne a ranar Asabar a matsayin martani kan ikirarin da Atiku ya yi kan zabin ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Action Congress a 2007.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku Da Wike: "Shedan Ya Shigo Jam'iyyar Mu", Jigon Jam'iyyar PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Yi Gargadi

Atiku da Tinubu.
Atiku Tantirin Maƙaryaci Ne, In Ji Tinubu, Ya Tona Abin Da Ya Faru Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi a 2007. Hoto: @hartng.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dan takarar shugaban kasar na PDP, a hirar da Arise TV ta fitar a ranar Juma'a, ya ce ya ki amincewa Tinubu ya yi masa takarar mataimaki saboda baya son tikitin musulmi da musulmi.

Amma, a martanin da ya yi cikin sanarwa da Tunde Rahman, hadiminsa ya fitar, dan takarar na APC ya ce ikirarin ba gaskiya bane.

Ya kara da cewa Atiku ne ya masa tayin takarar mataimakin shugaban kasar.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Progressives Congress Presidential Candidate, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce dukkan yan Najeriya su ji tausayi da bakin ciki ga dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party, Alhaji Atiku Abubakar.
"A yunkurinsa na matsanancin son ya ga ya ci zabe ta hanyar raba kan mutane da addini, Atiku ya mayar da kansa mai sharara karya a talabijin a idon kowa.

Kara karanta wannan

Yan Majalisu Biyu Da Dubbannin Yan Siyasa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Gangamin Atiku

"Mun yi bakin cikin ganin irin wannan mutumin ya yi nesa da gaskiya. Saboda tsananin son mulki, Atiku a shirye yake ya yi kowanne irin karya idan yana ganin za ta samar masa kuri'a daya," dan takarar na APC ya ce cikin sanarwar da hadiminsa Mr Tunde Rahman ya fitar.

A martanin da ya yi, Tinubu ya ce Atiku baya cikin wadanda suka kafa jam'iyyar AC kawai an bashi tikitin takarar ne saboda bukatar yakar kakagida da Obasanjo da PDP ta yi ga demokradiyar Najeriya.

"Ina tausayawa Atiku. Son mulkinsa yasa ya dena fadan gaskiya da abin da ya faru a baya. Mun kafa AC ba tare da saninsa ba. Lokacin da Obasanjo ya saka shi yin hijira daga PDP, mun tallafa masa ta hanyar bashi takara a AC a 2007.
"Bari in fayyace a fili cewa Atiku ya min tayin takarar mataimaki a 2007. Bari kuma in fada cewa addini na bai canja ba. Lokacin da ya min tayin, ni musulmi ne kuma na yi imanin ya san addini na a lokacin.

Kara karanta wannan

APC ta rikice, wasu 'yan takarar shugabancin sun yi bore kan kin mayar musu da kudin fom

"Lissafin Atiku da yaudara ba ta da wani alaka da addini ko kula da addini. Kawai hakan na da alaka da abin da muka gano na karancin dattaku da son makirci."

Tinubu ya bada misalin abin da ya faru a zaben 1993 yana mai cewa Atiku ba shi da matsala da tikitin musulmi da musulmi domin ya yi kokarin ganin MKO ya dauke shi a matsayin mataimaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164