2023: Muna Da Kyakkyawar Alaƙa, Na Ɗauka Ina Da Goyon Bayan Obasanjo, Atiku
- Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya sa a ransa cewa yana da goyon bayan tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo
- Tun bayan bayyana tsohon mataimakin shugaban a matsayin ɗan takarar PDP, rikici ya ɓarke tsakanin masu ruwa da tsaki
- Obasanjo na ɗaya daga cikin waɗan da basu goyon bayan Atiku, amma ya ce yana bukatar tsohon Uban gidansa
Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ranar Jummu'a ya ce ya ɗauka tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, yana goyon bayansa a babban zaɓen 2023.
Atiku ya yi wannan furucin ne yayin da yake amsa tambayoyi a wata hira da kafar talabijin na Arise TV, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Ya kasance mataimakin shugaban ƙasa a Najeriya tsakanin 1999 zuwa 2007 lokacin Obasanjo na matsayin shugaban ƙasa.
Da yake martani kan raɗe-raɗin basu ga maciji da tsohon shugaban, Atiku ya ce yana tare da Mista Obasanjo har bayan ya zama ɗan takarar jam'iyyar PDP.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Atiku ya yi alƙawarin cigaba da gini kan dumbin ayyukan raya ƙasa da tsohon shugaban ƙasa ya fara da zaran an rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.
Shin Atiku na bukatar goyon bayan Obasanjo?
Da yake tsokaci kan bukatar Obasanjo ya goya masa baya wajen cika burinsa, Atiku ya ce:
"Me zai sa na ƙi bukatar goyon bayansa? Shi fa tsohon mai gidana ne. Tabbas zan buƙaci cikakken goyon bayansa, na takaice muku ina tsammanin ina da goyon bayansa."
Tsayar da Atiku Abubakar, ɗan arewa a matsayin ɗan takarar kujera lamba ɗaya ya tayar da ƙura a cikin jam'iyyar PDP, inda wasu jiga-jigai ke ganin rashin adalci ne, ya kamata a maida takara hannun ɗan kudu.
EFCC ta bankaɗo yadda Dakataccen Akanta Janar ya karɓi Biliyan N15bn na goro don saurin biyan jihohi 9 wasu kuɗaɗe
Haka nan kuma matakin Atiku na zaɓar gwamna Okowa a matsayin abokin takararsa ya ƙara fusata mambobin jam'iyyar waɗan da ke ganin Gwamna Wike ya fi dacewa.
A wani labarin kuma Atiku ya ce ba ya tsammanin jam'iyyar LP zata ba da mamaci a zaɓen 2023 kamar yadda ake hasashe
Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ya ce baya tunanin Peter Obi zai kai labari a babban zaɓen 2023.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce ba ya ganin wani abun aljabi zai faru duba da kashi 90% na mutanen arewa ba su Soshiyal Midiya.
Asali: Legit.ng