Tsohon AGF Ya Karɓi Biliyan N15bn Don Gaggauta Biyan Jihohin Ɗanyen Mai Kuɗaɗensu, EFCC

Tsohon AGF Ya Karɓi Biliyan N15bn Don Gaggauta Biyan Jihohin Ɗanyen Mai Kuɗaɗensu, EFCC

  • EFCC ta ce dakataccen Akanta Janar, Ahmed Idris, ya karbi cin hancin biliyan N15bn don gaggauta biyan kashi 13% na raya yankunan da ake haƙo mai
  • Ana ware kaso 13% daga kuɗaɗen shiga na ɗanyen mai domin raya yankuna ta hannun gwamnatocin jihohi 9
  • A ranar Jumu'a 22 ga watan Yuli, 2022, Idris zai gurfana a gaban Kotun tarayya kan zargin almundahana da halasta kudin haram

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Akanta Janar na ƙasa (AGF) da aka dakatar, Ahmed Idris, ya karɓi biliyan N15bn ta bayan fage domin ya gaggauta biyan jihohi masu fitar da ɗanyen mai kason da ake ware musu.

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'adi (EFCC) ta ce dakataccen AGF ɗin ya karɓi kudin ne a matsayin toshiyar baki domin saurin tura wa jihohin guda 9 ƙaso 13% da ake ware musu.

Kara karanta wannan

Yadda na tsallake rijiya da baya lokacin harin yan ta'adda a Kuje, Abba Kyari ya magantu a Kotu

AGF, Ahmed Idris.
Tsohon AGF Ya Karɓi Biliyan N15bn Don Gaggauta Biyan Jihohin Ɗanyen Mai Kuɗaɗensu, EFCC Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa ƙaso 13% na kuɗaɗen da aka samu wata garabasa ce da tsarin rabo ya ware domin taimaka wa yankunan da ake haƙo ɗanyen mai su cigaba.

Kuɗaɗen na zuwa ne daga asusun tattara kuɗin shiga na tarayya zuwa yankunan ta hannun gwamnatocin jihohin su kamar yadda yake a sashi na 162 ƙarkashin sashi na 2 a kundin mulkin Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa johohi 9 da ke fitar da ɗanyen man fetur a Najeriya sun kasafta Biliyan N450.60bn daga asusun tarayya ta hanyar kaso 13% da ake ware musu a 2021.

Jihohin da ke shan wannan romon demokaraɗiyya sune: Delta, Akwa Ibom, Bayelsa, Ribas, Edo, Ondo, Imo, Legas da kuma Abia.

Yadda AGF ya karɓi cin hancin kuɗin

A cewar hukumar EFCC, Idris ya karɓi tukuicin N15,136,221,921.46 daga wurin Olusegun Akindele, domin ya taimaka wajen gaggauta tura wa jihohin kaso 13% da ake ware musu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Gwamna Matawalle ya haramtawa Sarakunan Zamfara naɗa Sarauta sai da sharaɗi ɗaya

Akindele ya kasance mai taimaka wa AGF ta ɓangaren fasaha daga watan Fabrairu zuwa Nuwamba na shekarar 2021.

AGF Idris zai gurfana gaban mai shari'a A.O. Adeyemi Ajayi, na babbar Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ranar Jumu'a, 22 ga watan Yuli.

A wani labarin kuma INEC ta gabatar da wani hukunci da take son a yi wa yan siyasa masu sayen kuri'u a Najeriya

Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta bukaci a samar da hukuncin haramcin shiga zaɓe na har abada ga duk wanda aka kama da sayen kuri'u.

Kwamishinan INEC na jihar Akwa Ibom, Mike Igini, ya ce ba Najeriya kaɗai haka ke faruwa ba, manyan kasashen duniya sun sha fama da matsalar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel