Sowore ya yi Karo da ‘Yan Takaran 2023, ya zargi Atiku, Obi da yaudarar mutane

Sowore ya yi Karo da ‘Yan Takaran 2023, ya zargi Atiku, Obi da yaudarar mutane

  • Omoyele Sowore ya yi wa Atiku Abubakar martani da yake maganar yadda zai gyara harkar wuta
  • Sowore yake cewa Atiku na da hannu wajen jawo tabarbarewar lantarki a gwamnatin Obasanjo
  • ‘Dan takaran na African Action Congress ya kuma caccaki abokin adawarsa a zaben 2023, Peter Obi

Abuja - ‘Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar African Action Congress, Omoyele Sowore, ya maida martani kan batun wutar lantarki.

Atiku Abubakar ya fito ya yi magana yayin da wutan lantarkin Najeriya ya samu matsala a ranar Laraba, abin ya yi sanadiyyar da aka shiga duhu.

Da yake magana a shafinsa na Twitter, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da lamarin, ya yi bayanin yadda zai shawo kan matsalar idan ya karbi mulki.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu ya magantu a kan manyan Bishop-Bishop da aka gani a wajen gabatar da Shettima

Amma Yele Sowore bai kyale Atiku ba, sai da ya yi masa raddi a shafinsa na Twitter.

Maganar da Atiku ya yi

A jawabinsa a Twitter, Atiku ya na cewa an sanar da shi wutan Najeriya ya samu matsala, ya ce wannan ne karo na shida a 2022 da wutar ta dauke.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Saboda muhimmancin lantarki, Atiku Abubakar ya ce zai kafa hukumar IDF wanda za ta nemo kudi domin gina abubuwan more rayuwa a kasar nan.

Atiku
'Dan Takaran PDP, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Sannan Atiku ya ce samar da wata hukumar IDCGA domin kwadaito masu zuba hannun jari.

Atiku bai damu da lantarki ba - Sowore

Yele Sowore yana ganin akwai rainin hankali tattare da alkawuran ‘dan takaran, ya ce a lokacin yana mataimakin shugaban kasa ne lamarin ya tabarbare.

“Wutan lantarkin Najeriya ya fara daukewa dif ne a lokacin kai da Obasanjo ku ka kashe $16bn, amma aka kare a duhu, gwamnatin Buhari karasa wa ta yi.”

Kara karanta wannan

Dan takarar APC Tinubu: Dole ne na kwaci Najeriya a 2023 don na samar da ayyukan yi

Alhaji Atiku, ka daina wata yaudara, ka na yi kamar ka damu da wutar Najeriya. #WeCantContinueLikeThis”

Sai yanzu Obi ya san da hakan?

Har ila yau, Legit.ng Hausa ta fahimci Sowore ya yi wa Peter raddi a dandalin Twitter. Hakan na zuwa ne bayan Obi ya koka kan yadda aka bar jama’a a duhu.

Sowore ya caccaki ‘dan takaran LP, yace ya taba zama Hadimin Goodluck Jonathan, kuma ya je Masar kwanan nan, amma ya na nuna sai yanzu ya gano haka.

Shari'a da Tinubu

An ji labari Lauyan Kungiyar Incorporated Trustees of Center for Reform and Public Advocacy ya yi nasara a kotu, Alkali ya amince da rokon da ya gabatar.

Kungiyar ta nemi Kotu ta matsawa Sufetan ‘Yan Sanda ya binciki Bola Tinubu bisa zargin yin karya a lokacin yana Gwamna, jiya kotu ta amince da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng