Rashin da'a: Mataimakan gwamna 5 da aka tsige su a Najeriya, amma kotu ta mayar dasu
A baya-bayan nan dai Najeriya ta shaida tsige mataimakan gwamnoni biyu: Rauf Olaniyan na jihar Oyo da Mahdi Aliyu-Gusau na Zamfara.
A makon nan, an tsige Olaniyan ne saboda ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC, kamar yadda Legit.ng Hausa ta ruwaito a baya.
Mataimakan gwamnoni a fadin Najeriya kadan ne suka fuskanci tsigewa kana suka samu damar komawa kujerunsu ta hanyar umarnin kotu.
Ga wasu da suka yi nasarar komawa kujerunsu a rahoton da muka tattara muku, kamar yadda The Nation ta kawo.
1. Eze Madumere
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Babbar kotun jihar Imo da ta yi zamanta a Owerri a ranar 25 ga watan Satumba, 2018 ta bayyana tsige Madumere a matsayin yunkuri mara tushe kuma hakan ba daidai bane a tsarin shari’a.
Mai shari’a Benjamin Iheaka, a hukuncin da ya yanke, ya tuhumi babban alkalin Imo, Paschal Nnadi da kuma babban mai shari’a na jihar, Militus Nlemadim kan kin bin tanadin sashe na 188(5) na kundin tsarin mulkin 1999 tare da trsige Madumere a ranar 31 ga Yuli, 2018.
2. Garba Gadi
Wata babbar kotun Bauchi a ranar 25 ga watan Yuni, 2010 ta bayar da umarnin mayar da marigayi Alhaji Garba Gadi kan kujerarsa ta mataimakin gwamnan jihar Bauchi.
An cire Gadi ne a ranar 13 ga Agusta, 2009 daga mukaminsa bisa zargin "rashin da'a".
Da yake yanke hukunci a kan lamarin, alkalin kotun, Mai shari’a Haruna Tsammani, ya ce tsige Gadi da majalisar ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa.
3. Peremobowei Ebebi
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Fatakwal a ranar 16 ga Fabrairu, 2011 ta dawo da Peremobowei Ebebi, tsohon mataimakin gwamnan jihar Bayelsa kan kujerarsa, wanda majalisar dokokin Bayelsa ta tsige a watan Yuni 2010.
An fara shari'ar Abba Kyari kan tuhumar safarar miyagun kwayoyi, NDLEA ta gabatar da shaida mai karfi a Kotu
Kwamitin daukaka kara ya yi la'akari da karar da Alex Iziyon, SAN, SAN, ya kawo mata a madadin mataimakin gwamnan da aka tsige bayan da babbar kotun jihar Bayelsa ta ki amincewa da hurumin shari'a kan lamarin.
Ebebi dai ya garzaya kotu ne domin nuna rashin amincewarsa da yadda aka tsige shi saboda a hangensa, hakan rashin bin ka’ida ne.
4. Ali Olanusi
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Akure, babban birnin jihar Ondo a ranar 24 ga Maris, 2017 ta lalata batun tsige tsohon mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Ali Olanusi.
Majalisar dokokin jihar Ondo ta tsige Olanusi wanda ya kasance mataimakin tsohon gwamnan jihar Dr. Olusegun Mimiko a shekarar 2015 bisa zarginsa da aikata rashin da'a.
Ya kuma shiga jam’iyyar APC jim kadan gabanin zaben shugaban kasa a shekarar 2015 kana kafin a tsige shi.
5. Sunday Onyebuchi
A ranar 18 ga watan Disamba, 2015 ne aka mayar da tsohon mataimakin gwamnan jihar Enugu Sunday Onyebuchi kan kujerarsa bisa hukuncin da babbar kotun jihar Enugu karkashin jagorancin mai shari’a Reuben Odugu.
Hukuncin dai ya soke tsige Onyebuchi tare da ba da umarnin maido masa duk wasu hakkokinsa tun daga lokacin da aka tsige shi daga kujerarsa zuwa lokacin da ranar da aka dawo dashi.
Majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin Eugene Odoh ta tsige shi ne a ranar 26 ga watan Agustan 2014 bisa shawarar wani kwamiti na mutum bakwai da jihar ta kafa.
Majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin Eugene Odoh ta tsige shi ne a ranar 26 ga watan Agusta, 2014, biyo bayan shawarar wani kwamitin mutane bakwai da babban alkalin jihar, Innocent Umezuruike ya kafa.
Kwamitin ya binciki zargin da gwamna Sullivan Chime ya yiwa mataimakin gwamnan ne na aikata halayen rashin da'a.
Yan majalisa 18 cikin 22 sun amince a tsige mataimakin gwamnan Zamfara, sun umurci Alkali ya fara bincike
A wani labarin, mutum 18 cikin 22 na mambobin majalisar dokokin jihar Zamfara sun amince da kudirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau.
Wannan ya faru ne kwanaki uku bayan majalisar ta aike masa da sakon tuhume-tuhumen da ake masa.
A zaman ranar Alhamis, mambobin majalisa uku basu halarta ba, rahoton Ptimes. Dan majalisa na jam'iyyar PDP, Salihu Usman (Zurmi ya gabas), kadai ne wanda bai amince a tsige Mahdi Gusau ba. R
Asali: Legit.ng