Tsohon Shugaban Kungiyar Kirstocin Najeriya, CAN, Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Gwamna a Najeriya
- An zabi Rabaran Joshua Olakunle, tsohon shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, matsayin dan takarar mataimakin gwamnan SDP a Kwara
- Rabaran Olakunle zai zama abokin takara ne ga Mr Hakeem Lawal wanda ya yi nasarar zama dan takarar gwamna na SDP a zaben fidda gwani da aka yi a watan Mayu
- Tsohon shugaban na CAN, kuma tsohon malami a Kwallejin Ilimi ta Kwara ya yi takarar majalisar jihar Kwara a karkashin jam'iyyun PDP da APC a baya
Kwara - An zabi tsohon shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, a Jihar Kwara, Rabaran Joshua Olakunle, a matsayin dan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben 2023, rahoton This Day.
Rabaran Olakunle wanda ya fito daga Ora a karamar hukumar Ifelodun, zai yi takara ne tare da Mr Hakeem Oladimeji Lawal, wanda ya yi nasarar zama dan takarar jam'iyyar a zaben cikin gida na ranar 31 ga watan Mayu.
2023: Sabon sabani ya kunno kai a APC kan wanda Tinubu ya zaba mataimaki, Gwamna El-Rufa'i ya fusata
Sanarwar da shugaban jam'iyyar SDP na jihar, Azeez Afolabi, ya fitar a Ilorin, ya ce dan takarar mataimakin gwamnan tsohon malamin jami'a ne kuma malamin addini, wanda ya zama babban lakcara a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara, Oro, kafin ya yi murabus a 2008.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar sanarwar, Olakunle ya yi digiri ta farko da na biyu a Jami'ar Ibadan a 1983 da 1988 sannan ya sake yin difloma a bangaren ilimi daga jami'ar Ilorin a 1994.
Sanarwar ta bayyana shi a matsayin "malamin makaranta kuma shugaban al'umma wanda ya yi wa kungiyoyin cigaban al'umma hidima a Kwara South da Igbomina."
Ya yi aiki a matsayin Minista a Cocin ECWA, Apapa, Lagos da Cocin ECWA a Agbeku a Ifelodun, Jihar Kwara kuma mamba ne mai karfi a Kungiyar Kirista ta Najeriya, CAN, da wasunsu.
Takaitaccen tarihin siyarsar Rabaran Olakunle
Ya fara siyasa ne a jam'iyyar SDP a 1993 daga baya ya koma jam'iyyar AD a 1999 kafin ya tafi Accord Party sannan jam'iyyar PDP inda ya yi takarar majalisar jihar Kwara a 2015.
Yana cikin wakilan PDP na kasa a taron gangami na 2015 ya sake takarar majalisar jihar Kwara a karkashin APC a 2019 lafin ya koma SDP a 2022.
Kazalika, sanarwar ta ce Rabaran Olakunle a matsayin dan takarar mataimakin gwamna zai kawo iliminsa, kwarewa a bangaren mulki, ayyukan al'umma da gaskiya wurin ceto jihar daga mummunan shugabanni idan aka zabe su a 2023.
Matasan Kirista a Najeriya Sun Bukaci INEC Ta Kara Tsawaita Kwanakin Rajistan Zabe
A wani rahoton, reshen matasa na Kungiyar Kirista ta Najeriya, YOWICAN, ta Arewa maso tsakiya ta yi roko ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, ta tsawaita kwanakin rajistan karin zabe don kada a dakilewa mutane damar yin zaben.
Allah kadai ke zabar wanda zai mulki al’umma, Ministan Buhari ya yi martani bayan APC ta sha kaye a zaben Osun
Owoyemi Olushola, Shugaban YOWICAN na Arewa maso tsakiya ne ya yi wannan rokon yayin taron manema labarai mai taken: "Ba mu amince da tikitin musulmi da musulmi ba" a ranar Talata a Abuja, rahoton NAN.
Asali: Legit.ng