Alkali ya halattawa Gwamnatin Ganduje karbo bashin Naira Biliyan 10 da ta yi niyya
- Babban kotun tarayya da ke zama a garin Kano, ya yi zama a kan shari’ar Gwamnatin Kano da KFF
- Kungiyar Kano First Forum ta na yunkurin hana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje karbo aron kudi
- Da aka koma kotu a makon nan, Alkali ya janye takunkuminsa, ya ce Gwamnatin za ta iya cin bashi
Kano – A makon nan, babban kotun tarayya da ke zama a Kano, ta saurari shari’ar da ake yi tsakanin kungiyar KFF da gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Daily Nigerian ta ce kotun tarayyar ta cire takunkumin da aka kakabawa gwamnatin Kano na karba bashin kudi har Naira Biliyan 10 da niyyar kafa na’urar CCTV.
Dr Yusuf Isyaka-Rabiu ya shigar da kara a madadin kungiyarsu ta Kano First Forum watau KFF, yana neman a haramtawa gwamnatin karbo aron wannan kudi.
Wadanda kungiyar KFF ta maka a kotu sun hada da Mai girma Gwamna Abdullahi Ganduje, da Kwamishinan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin Kano.
Sauran su ne Kwamishinan kudi, shugaban majalisar Kano, majalisar dokokin jihar, ma’aikatar kudi ta tarayya, ofishin DMO, hukumar FRC da kuma wani banki.
Da farko kotun ta bada umarni a dakatar da gwamnatin Kano daga cin wannan bashi da kafa na’urorin CCTV kafin a kammala sauraron lauyoyin duka bangarorin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma da aka koma kotu a makon nan, Alkali mai shari’a, Abdullahi Liman ya cire takunkumin da aka sa a ranar 1 a watan Yuli, a sakamakon sauraron lauyoyi.
An saurari Muhammad Dahuru
Tribune ta ce Lauyan gwamnatin jihar Kano, Muhammad Dahuru, ya roki Alkali ya janye hukunci da ya yi, ya ce hakan ya sabawa bukatar wanda yake karewa.
A ranar 7 ga watan Yulin nan, Dahuru ya shigar da kara, ya na neman alfarma wajen kotun, yana so a kyale wanda ake kara ya karbo bashin kudin da ya yi niyya.
An fara shari'ar Abba Kyari kan tuhumar safarar miyagun kwayoyi, NDLEA ta gabatar da shaida mai karfi a Kotu
Mai shari’a Abdullahi Liman ya amince da rokon Lauyan wanda ake kara, ya ce wadanda suka shigar da kara sun boye masa gaskiya tare da murda wasu bayanan.
Liman ya ce za a cigaba da shari’ar nan gaba domin Alkalan kotun tarayya za su tafi hutun shekara a ranar Juma'a. Nan gaba za a sanar da lokacin da za a sake zama.
Gwamnati v Abduljabbar
A jiya aka ji labari fitaccen Malamin nan, Abduljabbar Nasiru Kabara yana shari’a da Gwamnatin Kano da kuma kotun shari’a a Babban kotun tarayyan na Kano.
Dalhatu Shehu-Usman shi ne Lauyan da ya tsayawa malamin, yana so ayi watsi da shari’ar da ake yi, amma Alkali Abdullahi Liman ya ki amincewa da hakan
Asali: Legit.ng