2023: Ba don ra'ayin kaina na zabi Shettima ba, Tinubu ya fadi dalilin zabo mataimakinsa
- Tinubu zai gabatar da Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a gobe Laraba, 20 ga watan Yuli, a hukumance
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ce ya zabi tsohon gwamnan Borno a matsayin abokin tafiyarsa saboda goben yan Najeriya
- Kungiyar kamfen din Tinubu ta ce da ace tsohon gwamnan na Lagas ya yi la’akari da kabilanci da addini da bai zabo mataimaki daga marasa rinjaye a arewa ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi bayanin cewa ya zabi abokin takara daga cikin yan arewa marasa rinjaye ne saboda ci gaban kasar gabaki daya.
Tinubu ya bayyana hakan ne gabannin bayyana Alhaji Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a hukumance a ranar Laraba a Abuja, jaridar Independent ta rahoto.
Shettima: Yan Najeriya Sun Tattare Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Ke Kara Azama a Bangaren Fasaha
Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya ce da ace yana tunanin samun tarin kuri’u ta hanyar amfani da kabilanci ne toh zai zabi mataimaki daga yankin arewa maso yamma ne domin a cewarsa ita ce ta fi yawan masu rijistan zabe.
Hakazalika, dan takarar na APC ya ce abun da ya aikata babu bangarancin addini idan ba haka ba da ya zabi Kirista a matsayin abokin takara daga yankin da kiristoci suka fi yawa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wani jawabi daga kungiyar kamfen din Tinubu ya ce addini da kabilanci basa cikin lissafin APC da dan takararta Bola Tinubu wajen zabar abokin takara.
Kakakin kungiyar ta TCO, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa suna ta bibiyar zazzafar muhawarar da zabar Shettima ya haifar a kasar, Vanguard ta rahoto.
Kungiyar ta ce:
"Maimakon haka, ya zabo kwararren dan siyasa daga kabilar Kanuri marasa rinjaye daga arewa maso gabas.
Musulmi da Musulmi: Kada ku yarda wani fasto ko limami ya fada maku wanda za ku zaba, Keyamo ga yan Najeriya
"Abubuwan da ke gaba sune yadda za a tunkari tarin matsalolin da kasarmu ke fuskanta a yau: rashin tsaro, matsalolin tattalin arziki, kamar matsalar rashin aikin yi da ke addaban matasanmu.
“Dan takararmu ya zage damtse kan tarihin da ya kafa a Lagas wajen lashe zaben fidda gwanin APC da aka yi a watan Yuni da ya gabata. A matsayinsa na gwamna tsakanin 1999 da 2007, ya yi nasarar sauya jihar mara kyau zuwa ta hudu a karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika. Ya yarda cewa za a iya kwaikwayon abun da ya yi a Lagas a fadin Najeriya.”
Kungiyar ta kuma ce ya zabi Kashim Shettima wanda ya samar da ci gaba a jihar Borno a lokacin da yake matsayin gwamna duk da rikicin Boko Haram, don ya taimaka masa wajen ganin mafarkinsa ya zama gaskiya.
Atiku Abubakar na cikin koshin lafiya, in ji Mai magana da yawunsa
A wani labari na daban, kwamitin masu yada muradun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, sun yi watsi da jita-jitan da ake yadawa game da lafiyarsa, jaridar Vanguard ta rahoto.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai ba tsohon mataimakin shugaban kasar shawara kan harkokin labarai, Mazi Paul Ibe.
Kwamitin ta ce ta ga ya dace ne ta yi gyara ga wani rahoto da bidiyo da wasu makirai suka fitar inda suka nuna Atiku Abubakar cikin wani hali na rashin lafiya harma wani hadiminsa na taimaka masa wajen gyara zama a mota.
Asali: Legit.ng