Musulmi da Musulmi: Tinubu ya yi ganawar sirri da fitaccen fasto kan batun Shettima
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu na ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki gabanin zaben 2023
- An ruwaito cewa, dan takarar ya gana da wani fitaccen fasto kan batun da ya shafi tsayar da abokin takararsa wanda yake musulmi
- 'Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu tun bayan da Tinubu ya zabi Kashim Shettima a matsayin abokin takara
Jihar Osun - A yayin da ake ta cece-kuce kan tikitin takarar Musulmi da Musulmi na jam’iyyar APC gabanin 2023, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki, Bola Tinubu, ya gana da Fasto Enoch Adeboye na Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG).
Majiyoyin da suka zanta da jaridar This Day sun ruwaito cewa, an gana ne tsakanin Tinubu da Adeboye a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli a sansanin Redemption da ke jihar Ogun.
Shettima: Yan Najeriya Sun Tattare Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Ke Kara Azama a Bangaren Fasaha
Majiyar wadda ta nemi a sakaya sunanta ta kara da cewa uwargidan Tinubu, Sanata Oluremi ta halarci ganawar, inda ta kara da cewa tattaunawar sirrin ta yi tasiri matuka.
An ruwaito shi yana cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ya gana da Adeboye ranar Lahadi. Ganawar ta yi matukar tasiri. Shi (Adeboye) baya adawa da tikitin musulmi da musulmi”.
An kuma tattaro cewa daya daga cikin matakan da Tinubu zai dauka na gaba shi ne ganawa da shugabannin kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) kan wannan batu, Independent ta tattaro.
Jaridar ta bayyana cewa, Tinubu ya riga ya kafa wata tawaga ta wasu fitattun mutane da za su gana da shugabannin Kiristoci a jam’iyyar APC da kungiyoyin addini kamar CAN, Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN), da Cocin Katolika.
Manufar ita ce a yi kira ga wadannan kungiyoyi na addini da su fahimci tunanin tsohon gwamnan na Legas su kuma gane dalilin da ya sa ya zabi tsayar da tikitin musulmi da musulmi.
Tinubu ya dauki Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa
A wani labarin, rahotanni da ke zuwa mana a yanzu sun nuna cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives (APC) a zaben 2023, Bola Tinubu, ya bayyana abokin takararsa.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a babban zaben mai zuwa.
Tinubu ya sanar da hakan ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, a garin Daura, jihar Katsina, yayin da ya kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari gaisuwar ban girma na babban Sallah, Channels Tv ta rahoto.
Asali: Legit.ng