Sai da na binciki sama da mutane 20 kafin na zabi Idahosa – Kwankwaso

Sai da na binciki sama da mutane 20 kafin na zabi Idahosa – Kwankwaso

  • Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce sai da ya binciki sama da mutane 20 kafin ya zabi Idahosa a matsayin Abokin takarar sa
  • Rabiu Kwankwaso ya ce ya dauki Bishof Idahosa a matsayin abokin takarar sane saboda dinke barakar da Najeriya ke fama da shi
  • Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa Farfesa Rufa’i Alkali ya ce Kwankwaso da Idahosaza su ceto Najeriya daga kalubalen da ta ke fuskanta

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sen. Rabiu Kwankwaso, ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai cike da rudani, inda ya ce ya binciki mutane sama da 20 kafin ya dauki Bishof Isaac Idahosa a matsayin abokin takararsa.

Kwankaso ya ce:

“A yayin da muke neman abokin takara, mun binciki sama da mutane 20 da ke son tsayawa takara, wadanda dukkansu sun cancanci zama mataimakin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kaddamar da Mataimaki, ya ce ya dauko wanda za su gyara Najeriya

“Amma idan aka yi la’akari da barnan da aka yi wa kasar nan a shekarun baya, ya zama wajibi mu dauki abokin tafiya da zai dinke barakar da kasar ke fama dashi, wanda zai nuna adalci da jan kowa a jiki.
DAHOSA
Sai da na binciki sama da mutane 20 kafin na zabi Idahosa – Kwankwaso FOTO PM NEWS
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso, ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da Bishop Isaac Idahosa a matsayin abokin takararsa na zaben 2023 jiya a Abuja.

Kwankwaso ya bayyana Idahosa a matsayin mutum mai cikakken gaskiya, inda yace

“Na yi imanin za mu iya hada kai da gaskiya domin mu warkar da raunukan da aka yi wa kasar.”

A nasa jawabin shugaban jam’iyyar NNPP na kasa Farfesa Rufa’i Alkali ya ce tawagar za ta ceto Najeriya daga kalubalen da ta ke fuskanta.

Zaben Jihar Osun: 'Mun rungumi ƙaddara' - Adamu Abdullahi

A wani labari kuma, Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Senata Abdullahi Adamu, ya ce faduwar APC a zaben gwamnan jihar Osun jarrrabawa ce daga Allah. Rahoton BBC

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Abin Da Yasa Na Zabi Bishof Idahosa Matsayin Abokin Takara Na

Abdullahi Adamu ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da BBC HAUSA, inda yace:

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa