Yadda Shugaba Buhari ya jawo muka rasa zaben Gwamna a Jihar Osun - Jagoran APC
- John Mayaki yana ganin ba zai yiwu a wanke shugaban kasa daga rashin nasarar zaben Osun ba
- Jagoran na APC yana ganin Muhammadu Buhari ya taimaka wajen ba PDP nasara a zaben da aka yi
- Ana ji, ana gani ‘Dan takaran PDP, Ademola Adeleke ya tika Gwamna mai mulki a APC da kasa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Edo - Daya daga cikin manyan jam’iyyar APC a jihar Edo, John Mayaki ya zargi Mai girma Muhammadu Buhari da jawo masu rashin nasara a zaben Osun.
A karshen makon da ya gabata ne aka gudanar da zaben gwamna a jihar Osun inda APC ta sha kashi, John Mayaki yana ganin har da laifin shugaban kasa.
Daily Trust ta rahoto John Mayaki yana magana a game da zaben a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli 2022, inda ya nuna ‘ya ‘yan APC sun yi masu zagon-kasa.
A cewar Mayaki, Mai girma shugaban kasa ya yi watsi da APC a zaben, sannan ya kyale ‘yan jam’iyyar suka rika shirya mata makarkashiyar daga gida.
Muddin Muhammadu Buhari bai canza salonsa na kin kulawa da sha’anin jam’iyya ba, wannan zai iya jefa APC cikin matsala a zaben 2023, inji 'dan siyasar
Maganar da John Mayaki yayi
“Zagon-kasan wasu manyan ‘yan jam’iyya, gwamnoni da Ministoci a gwamnatin Muhammadu Buhari ya jawo rashin nasara a zabukan Edo da Osun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba ayi wa ‘yan jam’iyya sakayya, sannan ga ko-in-kular shugaban kasa, idan ba a dauki mataki kan wadannan ba, jam’iyyar APC za ta ruguje yana kallo.
A mulkin Buhari, Gwamnonin APC suka yi wa jam’iyya zagon-kasa a zaben Edo, yanzu ana zargin wasu a gwamnatinsa da hannu a rasa zaben jihar Osun.”
Allah jikan Obasanjo, ba don ya mutu ba
Duk da zagon-kasan da wasu a gwamnati suke yi, Mayaki ya ce shugaban kasa ba zai hukunta su ba.
Jaridar ta rahoto Mayaki yana mai cewa ya kamata shugannin jam’iyyar APC su yi koyi da Olusegun Obasanjo wanda ya yi mulki tsakanin 1999 da 2007.
Sai an yi gyara - Uche Nwosu
Vanguard ta rahoto Uche Nwosu, wanda jagoran APC ne a jihar Imo, yana cewa laifin shugabanni da rikicin gida da girman kai suka yi sanadiyyar rasa Osun.
Uche Nwosu ya fitar da jawabi yana mai cewa an yi watsi da tsofaffin ‘yan jam’iyya irinsu Rauf Aregbesola, ya ce dole sai an yi gyara kafin babban zabe na kasa.
Asali: Legit.ng