Allah kadai ke zabar wanda zai mulki al’umma, Ministan Buhari ya yi martani bayan APC ta sha kaye a zaben Osun

Allah kadai ke zabar wanda zai mulki al’umma, Ministan Buhari ya yi martani bayan APC ta sha kaye a zaben Osun

  • Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya yi shagube ga jam'iyyarsa ta APC bayan kayen da ta sha a zaben gwamnan jihar Osun
  • Aregbesola wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar, ya bayyana cewa Allah ne ke bayar da mulki ga wanda ya so
  • Ministan dai baya goyon bayan tazarcen gwamna mai ci, Gboyega Oyetola, inda har ya fito da dan takarar da yake so amma ya sha kaye a zaben fidda gwanin jam'iyyar

Osun - Jaridar The Cable ta rahoto cewa ministan harkokin cikin gida kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya yi martani kan kayen da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sha a zaben gwamnan jihar.

A ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli ne hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Ademola Adeleke, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan na Osun.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dan takarar PDP da ya lallasa APC a Osun ya yi martani bayan cin zabe

Rauf Aregbesola
Allah kadai ke zabar wanda zai mulki al’umma, Ministan Buhari ya yi martani bayan APC ta sha kaye a zaben Osun Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Dan takarar PDP ya samu kuri’u 403,371 wajen kayar da gwamna mai ci kuma dan takarar APC, Gboyega Oyetola, wanda ya samu kuri’u 375,027.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Aregbesola da Oyetola, domin ministan ya yi adawa da zarcewar gwamnan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ministan ya goyi bayan tsohon sakataren gwamnatin jihar, Moshood Adeoti amma sai Oyetola ya lashe tikitin jam’iyyar a zaben fidda gwani.

Bayan dan takarar da ya fi so ya sha kaye, Aregbesola ya nuna adawa da zaben fidda gwanin.

A yanzu haka APC a Osun ta rabu gida biyum – masu biyayya ga Aregbesola da masu goyon bayan Oyetola.

Ministan bai halarci gangamin yakin neman zaben APC a Osun ba wanda aka yi a ranar Talata, wanda Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar da sauran gwamnoni da manyan jam’iyyar suka halarta.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu : Atiku Ya Taya Adeleke Murnar Lashen Zaben Gwamnan Jihar Osun

Hakazalika bai kada kuri’a a zaben ba kuma wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa yana a kasar Jamus.

Duk da cewar baya nan a lokacin zaben, Aregbesola ya yi shagube ga jam’iyyarsa kan kayen da ta sha a Osun.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa sa’a daya bayan sanar da sakamakon ministan ya je shafinsa na Facebook inda ya wallafa sakon.

Ya nakalto shafi na hudu, aya ta 17 na littafin Daniel. Ministan ya rubuta cewa:

“Madaukakin sarki na mulki a cikin mulkin dan adam, sannan ya bayar da shi ga wanda ya ga dama.”

Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar Osun

A baya mun kawo cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP),Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Baturen zabe a jihar, Toyin Ogundipe, ne ya sanar da sakamakon zaben a safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar Osun

Adeleke ya samu kuri’u 403, 371 wajen lallasa babban abokin hamayyarsa Gboyega Oyetola na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ya samu kuri’u 375,027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng