21:14: Jihohin da APC da PDP ke mulka ya zuwa bayan zaben gwamnan jihar Osun
A ranar Asabar, 16 ga watan Yuli ne al’ummar jihar Osun suka fito kwai da kwarkwata domin kada kuri’a domin zabo wanda zai mulke su na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Da sanyin safiyar Lahadi 17 ga watan Yuli ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.
Adeleke ya karshen mulkin gwamna mai ci, Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC yayin da ya samu nasara a kananan hukumomi 17 cikin 30 na jihar, kamar yadda muka kawo a baya.
Nasarar da jam’iyyar PDP ta samu a Osun ya dan kawo sauyi salon siyasa domin kuwa a yanzu jam’iyyar ta adawa ta kara samun iko a jiha guda gabanin zaben 2023 mai zuwa.
A halin yanzu dai jam’iyyar APC mai mulki tana rike da jihohi 21 yayin da jam’iyyar adawa ta PDP ke rike da 14 ciki har da sabuwar jiharta ta Osun. Jihar Anambra ce kadai ke hannun jam’iyyar APGA mai alamar zakara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin jihohi da jam'iyyun da ke mulkarsu
- Abia - PDP
- Adamawa - PDP
- Akwa Ibom - PDP
- Anambra - APGA
- Bauchi - PDP
- Bayelsa - PDP
- Benue - PDP
- Borno - APC
- Cross River - APC
- Delta - PDP
- Ebonyi - APC
- Edo - PDP
- Ekiti - APC
- Enugu - PDP
- Gombe - APC
- Imo - APC
- Jigawa - APC
- Kaduna - APC
- Kano - APC
- Katsina - APC
- Kebbi - APC
- Kogi - APC
- Kwara - APC
- Lagos - APC
- Nasarawa - APC
- Niger - APC
- Ogun - APC
- Ondo - APC
- Osun - PDP
- Oyo - PDP
- Plateau - APC
- Ribas - PDP
- Sokoto - PDP
- Taraba - PDP
- Yobe - APC
- Zamfara - APC
Dan takarar PDP da ya lallasa APC a Osun ya yi martani bayan cin zabe
Jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Osun, dan takarar jam'iyyar PDP da ya lashe zaben ya yi martani mai daukar hankali
Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, ne ya fito a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala a jiya Asabar 16 ga watan Yulin 2022.
Da yake mayar da martani game da zabensa ta shafinsa na Twitter, Adeleke ya bayyana cewa, ya kawo haske ga jihar.
Asali: Legit.ng