Yanzu-Yanzu: Dan takarar PDP da ya lallasa APC a Osun ya yi martani bayan cin zabe
- A yau aka sanar da wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun da aka yi jiya Asabar 16 ga watan Yulin 2022
- Ademola Nurudeen Jackson Adeleke ya yi martani game da cin zabe da ya yi jim kadan bayan sanarwar INEC
- Ya zuwa yanzu dai jam'iyyar PDP ta kara samun jiha guda, yayin da APC ta rasa jihar guda, tana da jihohi 21
Jihar Osun - Jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Osun, dan takarar jam'iyyar PDP da ya lashe zaben ya yi martani mai daukar hankali.
Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, ne ya fito a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala a jiya Asabar 16 ga watan Yulin 2022.
Da yake mayar da martani game da zabensa ta shafinsa na Twitter, Adeleke ya bayyana cewa, ya kawo haske ga jihar.
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na kawo haske jihar Osun."
Jihohi da jam'iyyunsu: APC na da jihohi 21, PDP na da 14
Da sanyin safiyar Lahadi 17 ga watan Yuli ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.
Adeleke ya karshen mulkin gwamna mai ci, Gboyega Oyetola na jam’iyyar APC yayin da ya samu nasara a kananan hukumomi 17 cikin 30 na jihar, kamar yadda muka kawo a baya.
Nasarar da jam’iyyar PDP ta samu a Osun ya dan kawo sauyi salon siyasa domin kuwa a yanzu jam’iyyar ta adawa ta kara samun iko a jiha guda gabanin zaben 2023 mai zuwa.
A halin yanzu dai jam’iyyar APC mai mulki tana rike da jihohi 21 yayin da jam’iyyar adawa ta PDP ke rike da 14 ciki har da sabuwar jiharta ta Osun. Jihar Anambra ce kadai ke hannun jam’iyyar APGA mai alamar zakara.
Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar Osun
A wani labarin, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP),Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.
Baturen zabe a jihar, Toyin Ogundipe, ne ya sanar da sakamakon zaben a safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, jaridar The Cable ta rahoto.
Adeleke ya samu kuri’u 403, 371 wajen lallasa babban abokin hamayyarsa Gboyega Oyetola na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ya samu kuri’u 375,027.
Asali: Legit.ng