Yarinya ta tattara dukkan kudin da ta tara, ta ba Peter Obi domin kamfen dinsa

Yarinya ta tattara dukkan kudin da ta tara, ta ba Peter Obi domin kamfen dinsa

  • Wata yarinya mai matsakaicin shekaru ta sadaukar da dukkan kudaden da ta dadae tana tarawa ga Peter Obi domin ya cimma burinsa
  • Covenant Okereke ta garzaya har inda 'dan takarar shugabancin kasan na Labour Party yake, tare da mika masa kudin da ta dade tana tarawa
  • Tace bata nadama saboda ta san mutum nagari ta bai wa kudinta, kuma Ubangiji ne yayi mata jagorar domin taimawaka Obi

Enugu - Wata matashiyar budurwa mai suna Convenant Okereke ta sadaukar da dukkan kudinta ga 'dan takarar shugabancin kasa na Labour Party, Peter Obi.

Okereke tace wannan kyautatawar yana daga cikin kokarinta na taimakawa Obi domin cimma burinsa, jaridar Independent ta ruwaito.

Peter Obi
Yarinya ta tattara dukkan kudin da ta tara, ta ba Peter Obi domin kamfen dinsa. Hoto daga independent.ng
Asali: UGC

Ta bada tallafin ne a ranar Talata da ta gabata yayin da Obi ya ziyarci jihar Enugu domin tattaunawar kai tsaye da Urban Radio, wanda ke kan titin shugaban kasa, Independence Layout, Enugu.

Kara karanta wannan

2023: APC, PDP Na Fuskantar Babban Barazana A Yayin Da Peter Obi Ya Fara Kamfen A Arewa, Ya Ziyarci Dattijon Arewa Mai Karfin Fada A Ji

Matashiyar tace Ubangiji ne ya jagoranceta da ta taimaki Obi da 'dan kudinta wanda ta dade tana tarawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Dan takarar shugabancin kasan na Labour Party ya samu marabar girmamawa daga magoya bayansa bayan kammala shirin gidan rediyon, inda matashiyar ta tunkari 'dan takarar tare da mika masa kyautar.

Okereke tace ta dinga kokarin tara kudi kuma ta dinga addu'ar Ubangiji ya nuna mata mutum nagari wanda za ta bai wa kudin.

Yace "Ubangiji ya amsa addu'ata a yau. Gidanmu na wannan titin kuma naji zuwan Peter Obi gidan rediyon kuma na garzayo.
"Ina ta godiya ga Ubangiji da ya amsa addu'ata. Ina kokarin taimakawa mutum nagari duk da ban ware wanda zan bai wa ba," Okereke tace.

Dalilin da ya sa na yi tsallaken layi yayin kada kuri'a - Adeleke

A wani labari na daban, 'dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Ademola Adeleke, ya bayyana dalilin da ya sa ya tsallaken layi a rumfunan zaben sa domin kada kuri’arsa a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Takarar Tinubu-Shettima: Jami’an DSS sun ankarar da Buhari abin da suka hango

Rahoton PUNCH Da yake gabatar da tambayoyi daga ‘yan jarida kan dalilin da ya sa yayi tsallaken layi don kada kuri’a a gaban wadanda ya hadu da su a rumfar zabe, tsohon dan majalisar ya ce hakan ya faru ne saboda jama’a na kaunarsa.

Adeleke ya yaba da yadda hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta shirya zaben, ya ce tsarin INEC yayi da kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng